1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

sabon tsarin kula da lafiya a jamus

Zainab A MohammadSeptember 24, 2006
https://p.dw.com/p/Bu5L

Ministan kula harkokin lafiya na Jamus ,tace babu gudu babu jada baya a dangane tsarin da ta gabnatar na gyare gyare a harkokin kula da lafiya na wannan kasa,batu daya kawo rarrabuwar kawuna tsakanin wakilan gwamnatin hadin gwiwa,wanda kuma ya dasa ayar tambaya adangane da cigaban wannan gwamnati.

Tun a watan yuli nedai,Ministar kula da lafiya Ulla Schmidt,wadda ta fito daga jammiya SPD,ta gabatar da sabon tsarin harkokin kula da lafiya anan jamus,wanda shugabar gwamnati Angela Merkel,yar jammiyar masu raayin mazan jiya,taki amincewa dashi saboda matsaloli na kudaden tafiyar da sabbin tsarin.Babban abunda sabon tsarin ya kunsa dai ,shine mayar da harkokin kula da lafiya a karkashin cibiya gudatare da tsarin na SPD na bada gudummowan kashi daya daga cikin 100 na gwargwadon kudaden da kowane iyali ke samu.Hakan dai nufin,baa dorawa iyalai wadanda basa samun kudi masu yawa ba, kudaden kiwon lafiya.Adangane da hakane Schmitd tace ana iya ciga da tattauna yadda gwamnati zata dauki nauyin tafiyar da wannan tsari,amma bazaa soke shi ba.