Sabon tashin hankali tsakanin Isra′ila da Falasɗinawa | Siyasa | DW | 04.04.2013
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Siyasa

Sabon tashin hankali tsakanin Isra'ila da Falasɗinawa

Tsagaita wuta tsakanin Hamas da Isra'ila na cikin tangal-tagal, inda aka sake kai wa juna farmaki, bayan mutuwar wani ɗan Falasɗinu a gidan yarin Isra'ila

epa02717471 Handout picture released by the Hamas Press Office shows Palestinian president Mahmud Abbas (centre left) speaking with Hamas leader Khaled Meshaal (centre right) in Cairo, Egypt, 04 May 2011. Palestinian President Mahmoud Abbas, leader of the Fatah party, and Hamas leader Khaled Mashaal on 04 May shook hands in Cairo on a reconciliation deal which ended a bitter four-year-long dispute between the two largest Palestinian factions. It was the first time the two men had met since Hamas routed security officials loyal to Abbas and the Palestinian Authority and seized sole control of the Gaza Strip in June 2007. EPA/HAMAS PRESS OFFICE HANDOUT HANDOUT EDITORIAL USE ONLY

Mahmud Abbas da Chaled Meshaal a birnin Alƙahira

Sojojin Israila sun dau wannan mataki ne a matsayin martanin ga hare haren rokoki da Falasɗinawa suka rinka kaiwa akan kasarsu. To sai dai babu wanda ya jikkata a cikin wadannan hare haren, a safiyar jiya Laraba ne kuma aka fuskanci harbin rokokin cikin harabar Isra'ila abin da ya janyo fargabar sake barkewar yakin nan na yini takwas tsakanin kungiyar Hamas da sojojin Isra'ila a watan Nuwamban bara.

Stone-throwing Palestinian protesters take cover behind old doors during clashes with Israeli troops in the West Bank city of Hebron April 3, 2013. The death of Maysara Abu Hamdeya, a prisoner serving a life sentence over an attempt to bomb an Israeli cafe who died of cancer on Tuesday, touched a nerve among Palestinians, who regard their brethren in Israeli jails as heroes in the fight for statehood. REUTERS/Darren Whiteside (WEST BANK - Tags: POLITICS CIVIL UNREST)

Boren Falasdinawa agarin Hebron dake yammacin Kogin Jordan

Yan kasar Isra'ila guda shida da Falisdinawa 169 ne dai suka rasa rayukansu a wancan lokacin. Akan haka ne ma ministan tsaron Israila Moshe Yaalon ya mai da martani da cewa sojojin Israila ba za su zura ido su ga ana kai wa kasarsu hari ba. To sai dai akwai rahotannin marasa tabbas dake nuni da cewa wata kungiyar yan Salafiyya ta Falasdinawa ta yi ikirarin kai hare haren baya bayan nan. Su dai sojin Isra'ila suna dora alhakin hare haren ne akan kungiyar Hama dake da iko da zirin na Gaza, a cewa u ra'ayin aiwatar da tsagaita alhaki ne da ya rataya a wuyan Hamas. Sai da ma yan Salafiyyan suka karya yarjejeniyar tsagaita wutar.

Lokacin da Shugaba Barack Obama ya kai ziyara a wannan yanki a watan Maris suna masu kai hare haren akan birnin Sderot . Anis Mushin wanda dan jarida ne dake aiki da cibiyar nazarce nazarcen Falisdinawa dake birnin Beirut na kasar Libanion ya wanke Hamas daga hare haren baya bayan nan.

epa03647581 Palestinians take part a protest in the West Bank city of Nablus, 02 April 2013, after the news of the death of Maysara Abu Hamdiyeh in the Israeli Soroka hospital. Reports state that Maysara Abu Hamdiyeh died after being transfered from prison to Israel's Soroka Hospital after throat cancer has spread to his spinal cord. EPA/ALAA BADARNEH +++(c) dpa - Bildfunk+++

Hayaƙin sa ƙolla da sojan Isra'ila suka harbawa Falasɗinawa masu zanga zanga

" Yace Babu wata manufa da Hamas za ta cimma game da haka. Ita ce ke da ikon da zirin Gaza. A don haka tana bukatar tabbatar da zaman lafiya a wannan wuri. Sam ba ta bukatar ganin ana harba rokoki. Ba ta son sake ganin fushin Isra'ila"

Mushin ya kara da cewa Hamas ba ta dade da nada shugabanninta a don haka ba ta muradin danganta kanta da balallun kungiyoyi ko wasu kasashe ko kuma kungiyar Alka'ida dake da manufar yin kafar ungulu ga kwaryar kwaryar zaman lafiya da ake samu a wannan yanki.

Kungiyar Hamas a nata bangaren ta na nata kokarin dominn tabbatar da zaman lafiya. Shi dai dan jaridar ya nasabta hare haren baya bayan nan da mutuwar da wani ba-Falasdina a gidan yarin Israila . Ita kuma kungiyar Salafiyya da ta yi ikirarinn kai hare haren ta ce ta dau wanna mataki a matsayin fansa ga mutuwar da Maysara Abu Hamdiyeh mai shekaru 64 ya yi a ranar Talata bayan da ya yi fama da cutar sankarau.

A stone-throwing Palestinian protester kicks a tear gas canister fired by Israeli troops during clashes in the West Bank city of Hebron April 3, 2013. The death of Maysara Abu Hamdeya, a prisoner serving a life sentence over an attempt to bomb an Israeli cafe, from cancer on Tuesday, touched a nerve among Palestinians, who regard their brethren in Israeli jails as heroes in the fight for statehood. REUTERS/Ammar Awad (WEST BANK - Tags: POLITICS CIVIL UNREST)

Hotunan Maysara Abu Hamdiyeh, wanda mutuwar sa ta jawo boren Falasɗinawa

Mahukuntan Falasidunawa sun yi korafin cewa Abu Hamdiyeh ya mutu ne bayan da aka ki bashi kulawar da ta dace abin da ya janyio fushin Falasdinawa da kusoshin siyasarsu. To sai dai kakakin gidan yarin Isra'ila ya musunta wannan zargi. Shi kuma Yithak Reiter masanin kimiyar siyasa a Isra'ila na ganin cewa a baya ga Hamas akwai kungiyoyin Falasdinawa masu matsanancin ra'ayi da har ke rike da manufar harba rokoki cikin Israila, inda yace.

"Yace mai yiwuwa ne baicin Hamas akwai kungiyoyin Falasdinawa masu matsanancin ra'ayi dake kokarin yin kafar ungulu ga tattaunawar da za a yi tsakanin Israila da Hamas a birnin Alkahiran Masar nan gaba.

Masanin yace to amma bai sani ba ko da wani kyakkyawan sakamako da za a samu daga shirin ministan harkokin wajen Amirka John Kerry na kai ziyara a cikin makonni biyu a yankin Gabas ta Tsakiya domin samar da kusantar da juna tsakanin Falasɗinawa da Isra'ila.

Mawallafa: Andreas Gorzewski / Halima Balaraba Abbas

Edita: Usman Shehu Usman

Sauti da bidiyo akan labarin