Sabon takunkumi ga Rasha | Labarai | DW | 21.06.2014
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Sabon takunkumi ga Rasha

Ƙasashen Jamus da Amirka da kuma Faransa sun yi barazanar sake ƙaƙabawa ƙasar Rasha takunkumi in har ba ta kawo ƙarshen rikicin da ake fama da shi a Ukraine ba.

Ƙasashen na yamma dai na zargin Rashan da iza wutar rikicin na gabashin Ukraine da ke neman zama ƙadangaren bakin tulu. Shugabannin ƙasashen uku sun tattauna ne ta wayar tarho inda suka cimma yarjejeniya kan cewa in har Moscow ba ta ɗauki ko wane mataki ba wajen kawo ƙarshen rikicin, Amirka da Ƙungiyar Tarayyar Turai wato EU za su ɗauki matakan sake sanya mata sabon takunkumi.

Amirkan dai na zargin mahukuntan Moscow da yunƙurin bai wa 'yan awaren gabashin Ukraine ɗin tankokin yaƙi da kuma jibge dakarun Rashan a daf da kan iyakar ƙasashen biyu da nufin kafa sansanin soja a wajen.

Mawallafiya: Lateefa Mustapha Ja'afar
Edita: Abdourahamane Hassane