Sabon sumamen ′yan sanda a Mombasa | Labarai | DW | 19.11.2014
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Sabon sumamen 'yan sanda a Mombasa

Jami'an 'yan sanda na kasar Kenya sun sake kai wani sabon sumame a wani masallaci da ke birnin Mombasa, inda suka samu makamai da dama.

Wannan ya zo ne kwanaki biyu kacal bayan wani sumaman da jami'an tsaron suka kai a masallatai biyu na birni na Mombasa inda ake zargin mutanen da hada baki da masu tayar da kayar baya na kungiyar Al-Shabaab a cewar wata majiya ta 'yan sandar kasar.

A lokacin da ya ke bayani ga manema labarai, Richard Ngatia, Shugaban 'yan sanda na unguwar Kisauni, inda aka kai wannan samame, ya tabbatar da cewa sun dauki wannan mataki, amma kuma ya ce sai nan gaba zasu bayar da dalillan yin hakan.

Sai dai a cewar wani jami'in 'yan sandar da bai so a bayyana sunansa ba, an samu makammai, da ma wasu bama-bamai da gurneti masu yawa a wannan sumame.

Mawallafi: Salissou Boukari
Edita : Mouhamadou Awal Balarabe