Sabon shugabanci cikin jam′iya ɗaya tilo a China | Siyasa | DW | 07.11.2012
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Siyasa

Sabon shugabanci cikin jam'iya ɗaya tilo a China

Kimanin wakilai 2200 ke halartar babban taron jam'iyar kwaminis karo na 18 a birnin Beijing, inda a ƙarshe za a zaɓi sabbin shugabanninta.

A ranar Alhamis takwas ga watannan na Nuwamban jam'iyar Kwaminis ta ƙasar China ke fara babban taronta karo na 18. Bayan shekaru biyar jam'iyar mai membobi miliyan 80 kuma ke matsayin wata jam'iyar siyasa mafi girma a duniya, ke gudanar da babban taronta, inda take zaɓen sabbin shugabanninta.

Wannan babban taron kuwa karo na 18 na jam'iyar ta 'yan kwaminis a China na da muhimmanci a fagen siyasar duniya saboda ƙarfinta a faɗin ƙasar dake matsayi na biyu a ƙarfin tattalin arzikin duniya, kana a ƙarƙashinta rundunar sojin ƙasar ta ke, kuma a gun wannan taron za a canza shugabanninta da ma na ƙasar baki ɗaya.

Sarkakiya a tsarin canza shugabanci

Fasalin canza shugabanni a cikin wani tsari na kama karya wani lamarin ne na siyasa mai ɗaure kai. A rubuce tsarin jam'iyar ya tanadi zaɓan shugabannin jam'iyar daga ƙasa zuwa sama. Wato wakilai 2200 na babban taron za su zabi wani kwamitin tsakiya mai membobi 350 wanda shi kuma a nasa bangaren zai zabi mutane 25 da za su jagoranci bangaren siyasa, wanda daga cikinsa shugabannin siyasa tara da za su fito, ciki har da babban sakataren jam'iya, shugaban jam'iya wanda shi ne shugaban kasa sai kuma firaminista. Sai dai a aikace shugabannin jam'iyar ke naɗa wakilan kwamitin tsakiya sannan jam'iyar ta albarkace su.

Xi Jinping

Xi Jinping, mutumin da zai ɗare kujerar shugabancin China

Sabon shugaban jam'iyar Xi Jingping shi ne zai gaji shugaba Hu Jintao, sai dai kawo yanzu ba a san irin alkiblar siyasar ba, duk da cewa ya kwashe shekaru biyar a matsayin matakin shugaban kasa. Sai dai a wani jawabi da yayi lokacin wata ziyara a Amirka, Xi ya ba da mamaki inda yayi magana a kan batun 'yancin ɗan Adam a China.

"Ina mai jaddada cewa China ta samu ci-gaba a fannin kare haƙƙin ɗan Adam ckin shekaru 30 da suka wuce. Sai dai har yanzu da sauran aiki gabanmu. Gwamnatin China na da babban kalubale gabanta wajen idan ana maganar inganta rayuwar jama'a da kuma haƙƙin ɗan Adam."

Kyakkyawar alaƙa da masu ruwa da tsaki

Shi dai Xi Jingping yana kyakkyawar dangantaka da sauran 'ya'yan jam'iyar, kasancewa ya fara yin suna ne a cikin rundunar soji yana ɗasawa da sojojin ƙasar kana kuma yana samun goyon bayan masu sassucin ra'ayi.

Deutschland China Wirtschaft Li Keqiang in Berlin

Li Keqiang ɗan lelen shugaba Hu Jintao

Wataƙila wannan shi ne dalilin da ya sa ya ka da Li Keqiang lokacin da ake wa shugabancin jam'iyar kwaswkarima. Shi dai Li Keqiang dake zama ɗan lelen shugaba mai ci Hu Jintao, shi zai rike mukamin firaminista karkashin shugaba Xi.

Li kamar Hu ya fito ne daga lardin Anhui dake tsakiyar kasar ta China, a can kuma ya fara siyasa a reshen matasa na jam'iyar kwaminis. A cikin shekarun baya bayan nan ya yi tafiye tafiye a kasashe kawayen China. Ya nakalci siyasar duniya. A wani jawabi da yayi a jami'ar Hong Kong ya ba da mamaki inda ya yi jawabinsa cikin turanci.

"Jami'ar Hongkong, jami'a ce da aka gina ta saboda China da kuma duniya. Ta zama babbar makarantar neman ilimi mai zurfi a China. Tana taka muhimmkiyar rawa a ci-gaban China da kuma haɗakar ta da duniya."

Abin jira a gani shi ne mutane za su dafa wa sabon shugaban kasa kuma shugaban jam'iyar Xi Jingping da sabon firaminista Li Keqiang baya. Sunayensu za su bayyana ne a taron manema labarai da za a yi bayan babban taron na jam'iyar ta 'yan Kwaminis a China.

Mawallafa: Matthias von Hein / Mohammad Nasiru Awal
Edita: Yahouza Sadissou Madobi

Sauti da bidiyo akan labarin