Sabon shugaban Tunisiya zai kama aiki | Labarai | DW | 29.12.2014
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Sabon shugaban Tunisiya zai kama aiki

Za a rantsar da sabon Shugaban Tunisiya ranar Laraba mai zuwa

Jami'an kasar Tunisiya sun bayyana cewa za a rantsar da sabon Shugaban kasar da aka zaba Beji Caid Essebsi jibi Laraba, yayin wani biki a majalisar dokokin kasar.

Caid Essebsi dan shekaru 88 daga jam'iyyar masu adawa da hada addini da siyasa, ya kada shugaba mai barin gado Moncef Marzouki, abin da kasashen duniya suka yaba da irin ci-gaban siyasa da aka samu, shekaru kusan hudu bayan juyin-juya halin da ya kawo karshen gwamnatin kama karya ta Zine El Abidine Ben Ali. Lamarin da ya zama mafarin juyin-juya hali a wasu kasashen Larabawa.

Mawallafi: Suleiman Babayo
Edita: Zainab Mohammed Abubakar