Sabon shugaban kasar Malawi ya kama ragamar aiki | Labarai | DW | 02.06.2014
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Sabon shugaban kasar Malawi ya kama ragamar aiki

Sabon shugaban Malawi Peter Mutharika ya ce zai mayar da hankali wajen bunkasa tattalin arziki da hadin kan kasa

A wannan litinin an kaddamar da sabon shugaban Malawi Peter Mutharika wanda a karshen mako hukumar zabe ta tabbatar da zaben da aka yi masa a matsayin wanda zai jagoranci kasar da ke yankin kudancin Afrika.

Kimanin magoya bayansa 30,000 ne suka halarci bikin, wanda aka yi a filin wasa na tunawa da Kamuzu da ke birnin Blantyre cibiyar kasuwancin kasar. Mutharika ya kada tsohuwar shugaba Joyce Banda, kuma shi dan-uwa ne wa tsohon Shugaba Bingu wa Mutharika.

Sabon shugaban kasar ta Malawi Peter Mutharika yayin jawabin fara aikinsa ya ce zai ba da fifiko wajen daidaita tattalin arziki da hadin kan kasar.

Mawallafi: Zainab Babbaji Katagum
Edita: Mouhamadou Awal Balarabe

  • Kwanan wata 02.06.2014