Sabon shugaban BP | Labarai | DW | 27.07.2010
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Sabon shugaban BP

Baarmirke Robert Dudley zai maye gurbin ɗan Birtaniya Tony Hayward a shugabancin BP daga watan oktoba mai zuwa.

default

Robert Dudley

Shugaban kamfanin haƙo mai na Birtaniya ya yi murabus daga muƙaminsa, biyowa bayan suka da ya ke fiskanta game da malalar mai a tekun Mexico. Wannan matakin Tony Hayward ya ɗauke shi, domin kawon ƙarshen riƙon sakainar kashi da aka zarge shi da yi ma gurɓatar mashigin ruwan Amirka da malalar ta mai ta haifar.

Kamfanin haƙo man na ƙasar ta Birtaniya ya sanar da tafka asarar miliyan dubu 17 na dalar Amirka, tun bayan fashewar sunduƙi da ya yi sanadiyar kwararar miliyoyin gangunan ɗanyen mai a tekun Mexico. Tuni kamfanin ya sanar da Robert Dudley wanda ba´amirke ne a matsayin wanda zai maye gurbin Tony Hayward a muƙamin shugaban na BP. Mista Dudley, shi ne mutumin farko da ba ɗan Birtaniya ba da zai riƙe wannan muƙami.

Mawallafi: Mouhamadou Awal

Edita: Yahouza sadissou