1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Nadin sabon shugaban hukumar zabe a Tarayyar Najeriya

Ubale Musa / LMJOctober 21, 2015

Majalisar magabatan Tarayyar Najeriya ta amince da nadin shugaba da kuma mambobin hukumar zaben kasar mai zaman kanta wato INEC.

https://p.dw.com/p/1Gs6B
Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari
Shugaban Najeriya Muhammadu BuhariHoto: picture-alliance/AP Photo/C. Owen

A wani zaman gaggawa da suka gudanar a wannan Laraba a Abuja, majalisar ta baiyana Farfesa Mahmud Yakubu daga jihar Bauchi a matsayin mutumin da zai jagoranci harkokin hukumar har na tsawon wasu shekaru biyar. Sauran mabobin hukumar dai sun hada da Hajiya Amina Zakari da har ya zuwa yanzu ke zaman shugabar riko, a matsayin wakiliyar sashen Arewa maso Yamma da kuma Dr Anthonia Taye Okosi Simbine daga Kogi a matsayin wakiliyar Arewa ta Tsakiya. Sauran sune Alhaji Baba Shettima Arfo daga Borno wakilin Arewa maso Gabas da Dr Mohammed Mustapha Lecky daga jihar Edo wakilin Kudu maso Kudu. An kuma nada Mr Soyebi Adedeji Solomon a matsayin wakilin Kudu maso Yamma da Mr Lawrence Nwaruku wanda zai ci gaba da rike matsayinsa na wakilin Kudu maso Gabas. Aminu Waziri Tambuwal gwamnan jihar Sokoto ne ya sanar da sabbabin sunayen, Ya kuma yi wa wakilinmu na Abuja Ubale Musa karin haske kan dalilin da ya sanya Shugaba Muhammadu Buhari na Najeriyar ya nada wadannan mutane a fadarsa, wanda ya ce kundin tsarin mulkin kasar ya ba shi damar yin hakan.