Sabon shiri kan tarihin Afirka ga matasa | Zamantakewa | DW | 08.01.2018
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Zamantakewa

Sabon shiri kan tarihin Afirka ga matasa

Wannan shirin DW mai suna "Tushen Afirka" na amfani da majigi da rahotannin rediyo wajen bayyana siffofi 25 na mutanen da suka taka rawa a tarihin Afirka ciki har da Bayajida na Najeriya.

Wannan sabon shirin DW kan "Tushen Afirka" ga matasan nahiyar na amfani da majigi da rahotannin rediyo wajen bayyana siffofi 25 na mutanen da suka taka rawa a tarihin Afirka. Gidauniyar Gerda Henkel ce ta dauki nauyin shirin da aka kaddamar ranar Litinin 8 ga Janairu 2018 cikin harsunan Ingilishi, Amharik, Hausa, Kisuaheli, Faransanci da kuma harshen Portugal.

 Shirin na bayani dalla-dalla kan mutanen da tarihi ba zai taba mantawa da su ba kama daga Dinknesh, "Uwar al‘uma" da ta fito daga Habasha, hada da gwarzayen shugabanni na tsakiyar zamani kamar Sunjata Keita na Mali, i zuwa ga masu fafutukar neman 'yancin kai kamar Patrice Lumumba.

Muna amfani da majigin bidiyo  - wanda dan Najeriyan mai suna "Comic Republic" - ya zana a kan shafinmu na Facebook. Dama kafar sada zumunta na Facebook na gidan watsa labaran duniya na Jamus na da masu biya fiye da mutane miliyan hudu. Sannan a lokaci guda, muna watsa makamacin wannan shirin a kafar rediyo a kan wannan batun. A wannan kafa dai DW na da masu saurare kimanin  mutane miliyan 40 a kowane mako.

DW African Roots- Bayajidda (Comic Republic)

Bayajidda tushen sarautar Hausa bakwai

Ma'abota tashar DW sun nunar da cewar a mafi yawan lokuta ana bada tarihin Afirka ne ta fuskar kasashen da suka yi musu mulkin mallaka. "Matasan Afrika ba su da damar yin amfani da takardun tarihi," in ji Anna Brown a tsokacin da ta yi a Facebook. Wannan rata ce shirin "Tushen Afirka" ke neman cikewa. Sassa Afirka na DW sun dogara kan majiyoyi masu tushe ta Afirka, tare da hada gwiwa da masana tarihi, da al'adu da marubuta na Afirka don gudanar da aikin. Kuma ya fi raja'a kan matasan kasancewa sun fi kowa yawan a nahiyar.

"Batutuwa kan tarihin Afirka na matukar daukar hankali a ayyukanmu," a cewar Claus Stäcker, Darektan sashen Afirka na DW wanda kuma ya assasa shirin. Ya kara da cewa "Musamman ma matasa na kokawa game da yadda ake koyar da tarihin Turai, da kuma karancin abin da suke koya game da 'yan Afirka."

"Gidauniyar Gerda Henkel na goyon bayan ayyukan bincike daban-daban a Afirka, wadanda suke neman kareda adana rubuce-rubuce da tarihi" a cewar Michael Hanssler, Shugaban wannan gidauniya. "Labarin nahiyar, wanda ‚yan nahiyar ke bayarwa, don gabatar wa matasa - wannan ne tunanin na 'Tushen Afirka ' da gidauniyar ke goyon baya."

Shirin "Tushen Afirka" zai rika zuwa muku ranar Alhamis da rana, sannan a maimatashi ranar Lahadi a shirin rana.