Sabon sarkin Kano kalubale ga Jonathan | Afirka a Jaridun Jamus | DW | 13.06.2014
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Afirka a Jaridun Jamus

Sabon sarkin Kano kalubale ga Jonathan

Tun a matsayin shugaban babban bankin Najeriya Mallam Sanusi Lamido Sanusi ya ba wa gwamnati haushi, a yanzun ma haka ba zai canja ba a matsayin sarkin Kano.

Bari mu fara da jaridar Die Tageszeitung wadda ta yi tsokaci game da nadin tsohon gwamnan babban bankin Najeriya Mallam Sanusi Lamido Sanusi a mukamin sabon sarkin Kano.

Ta ce a matsayin shugaban babban bankin Najeriya Mallam Sanusi Lamido ya ba wa gwamnati haushi, a yanzun ma haka ba zai canja ba a matsayin sarkin Kano mafi yawan Musulmai a Najeriya. Bisa ga dukkan alamu kuwa nadin na sa na zama wani kalubale ga shugaba Goodluck Jonathan. A matsayin gwamnan babban bankin na Najeriya Mallam Sanusi Lamido ya taka muhimmiyar rawa wajen tsabtacce tsarin bankunan kasar. Kasancewarsa masanin kimiyyar tattalin arziki da dokar shari'ar Musulunci sabon sarkin na Kano wanda shugaban Najeriyar ya dakatar da shi daga mukamin shugaban babban bankin kasar a karshen watan Fabrairu, yanzu yana rike da wata sarautar gargajiya mai karfi, kuma bisa ga dukkan alamu wannan ka iya zama wani rauni ga shugaba Jonathan, domin sarkin Kano shi ne na biyu mafi girma bayan sarkin Musulmi a arewacin Najeriya. Bugu da kari masautar na da dangantaka ta kut da kut da siyasar kasar.

Afirka na da damammaki ga tattalin arziki

Kamfanonin Jamus na guje wa nahiyar Afirka duk da dinbim arzikin wannan nahiya inji jaridar Der Tagesspiegel.

Ta ce: A duk lokacin da aka ambato Afirka abin da ke zuwa kan kamfanonin Jamus shi ne yake-yake, cututtuka, cin han ci da rashawa, bisa wannan dalili ne huldar ciniki tsakanin Jamus da Afirka ba ta da yawa. Sai dai masana na ganin Afirka ba kawai arzikin danyun kaya take da shi ba, tana kuma zama wani yanki mai alfanu ga tattalin arziki musamman bisa la'akari da damar kafa kamfanoni da kuma samun kasuwanni masu riba a can.

Kare gandun daji da ke zama gida ga birrai

Bildergalerie Virunga-Park Demokratische Republik Kongo

Gandun dajin Virunga a Demokradiyyar Kongo

Bisa matsin lamba daga masu fafatukar kare muhalli kamfanin Soco daga Ingila ya dakatar da aikin neman danyan man fetir a gandun dajin Virunga da ke jamhuriyar Demokradiyyar Kongo, inji jaridar Die Tageszeitung.

Ta ce za a ci gaba da kare gandun dajin na Virunga da ke zama gida ga gwaggon birrai da ba safai ake samusu a wasu wurare ba, daga kamfanin hako man fetir. Godiya ta tabbata ga reshen kare dazuzzuka na asusun kare namun dawa wato WFF, yanzu kamfanin ya kawo karshen aikin neman danyan man fetir a dajin na Virunga. Wannan ya kawo karshen takaddamar tsawon shekaru. A shekarar 2002 gwamnatin shugaba Joseph Kabila ta raba yankin kan iyakarta da Yuganda gida biyar don tafiyar da aikin neman danyan man fetir ciki har da dajin na Virunga wanda aka hasashe yana kunshe da arzikin man fetir.

Kwararrun masu horas da 'yan wasa a Afirka

Interaktiver WM-Check 2014 Trainer Ghana Appiah

Coachin Ghana Kwesi Appiah

Ita kuwa jaridar Süddeutsche Zeitung ta mayar da hankali ne a kan gasar kwallon kafar duniya tana mai cewa mai horas da 'yan wasan kwallon kafar kasar Ghana Kwesi Appiah ya tabbatar wa duniya cewa Afirka ma na da kwararrun masu horas da 'yan wasan kwallon kafa. Ta ce shi dai Appiah mutum ne mai natsuwa wanda 'yan wasan kasar ke girmamawa, bai taba buga kwallo ko horaswa a waje karkashin wani kwantaragi ba, amma ya nakalci wasan kwallon kafa. Irin natsuwar da yake da ita da kuma salon horaswarsa ya sa ya samu karbuwa wajen 'yan wasan kasarsa. Hakan kuwa ka iya yin kyakkyawan tasiri a wasan da Ghanar za ta yi a Brazil.

Mawallafi: Mohammad Nasiru Awal
Edita: Umaru Aliyu