Sabon salon magudin zabe a Afirka | Afirka a Jaridun Jamus | DW | 09.08.2013
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Afirka a Jaridun Jamus

Sabon salon magudin zabe a Afirka

Jam'iyyu masu karfi na amfani da masana ilimin komfuta suna sauya sakamakon zabe ko kuma yawan mutanen da suka jefa kuri'a ba tare da an gane ba.

Bari mu fara da jaridar Neue Zürcher Zeitung wadda ta buga labari kan irin rawar da kwararrun masana ilimin komfuta ke takawa wajen magudin zabe a nahiyar Afirka. Ta ce ra'ayin masu sanya ido a zabuka a Afirka ya zo daya cewa an samu ci-gaba a zabukan da aka gudanar a kasashen biyu. A Kenya a shekarar 2008 'yan bangar siyasa sun kashe mutane 1500 domin taimaka wa wasu 'yan siyasa darewa kan karagar mulki. Jim kadan bayan haka jam'iyar ZANU-PF ta shugaban Zimbabwe Robert Mugabe ta tursasa wa 'yan adawa inda ta hana kada kuri'unsu inda rahotanni suka ce mutane 400 aka kashe a wanca lokaci. A kasashen biyu an sake gudanar da zabuka a wannan shekara, a Kenya a cikin watan Maris sai kuma a Zimbabwe a kwanan nan, duka zabukan sun gudana cikin kwanciyar hankali da lumana. Hakan ya samu ne saboda canja salon magudin zabe daga mazabu da tashoshin zabe zuwa kan na'urar komfuta, inda jam'iyyu masu karfi ke amfani da masana ilimin fasahar komfutar suna sauya sakamakon zabe ko kuma yawan mutanen da suka jefa kuri'a. A Kenya masu fasahar sun kutsa cikin taskar adana bayanai a komfutar hukumar zaben kasar suka canja yawan wadanda suka kada kuri'ar. Sannan a Zimbabwe dan uwa shugaba Mugabe ne ke sanya ido a kan rajistar masu zabe, wanda a bangrensa ya ba wa wani kamfanin Isra'ila kwangilar tsara rajistar. Ko da yake da farko kamfanin ya musanta zargin da aka masa na aikata zamba, amma daga baya ya amsa cewa ya aikata abin da aka biya shi da yi ne. Da yake wadannan abubuwan na faruwa ne a bayan idon masu sanya ido a zabe, to ke nan ya zama wajibi nan gaba a rika saka masana ilimin zakulo bayanai ta komfuta a cikin tawagogin masu sa ido a zabe na kasa da kasa.

Tababa game da sakamakon zaben Zimbabwe

Ita kuwa jaridar Süddeutsche Zeitung sharhi ta rubuta game da zaben Zimbabwe tana mai cewa an dauki kwanaki kafin gamaiyar kasa da kasa ta nuna damuwa game da nasarar lashe zaben da Mugabe ya yi. Da farko dai hankalin duniya ya kwanta kasancewa zaben na Zimbabwe ya gudana ba tare da wani tashin hankali ba. Amma yanzu kasashen yamma sun yi suka game da aringizon kuri'u da kura-kurai da aka tabka lokacin zaben. Saboda haka sun nuna shakku game da sahihancin sakamakon zaben. Wannan suka daga Washington da London da kuma Brussels ba za ta damu shugaba Mugabe mai shekaru 89 da haihuwa, domin zaben ya samu yabo daga tarayyar Afirka.

Gobara ta janyo cikas ga zirga-zirgar jirgin sama

Harkokin sun tsaya cak a filin jirgin sama mafi muhimmanci a gabacin Afirka dake zama mazaunin kamfanin zirga-zirgar jiragen saman Kenya Airways dake bunkasa yanzu, inji jaridar Frankfurter Allgemeine Zeitung tana mai nuni da gobarar da ta tashi a filin jirgin saman birnin Nairobin Kenya a ranar Laraba. Wannan lamarin ya auku ne a ranar da aka cika shekaru 15 da kai hare-haren ta'addanci kan ofisoshin jakadancin Amirka a Nairobin da kuma birnin Dar es Salaam na Tanzaniya, ya kuma uku ne a cikin wannan wata na Agusta lokacin da 'yan yawan shakatawa daga Turai da kuma Amirka ke bi ta Nairobi a hanyar zuwa yankunan da aka kebe namun dawa na Kenya.

Mawallafi: Mohammad Nasiru Awal
Edita: Umaru Aliyu