1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
SiyasaAfirka

Tashin hankali na fadada a yankin Ingilishi na Kamaru

January 9, 2021

Mayakan 'yan a ware na Ambazoniya na fadada kai ayyukansu zuwa bangaren masu magana da turancin Farasanci.

https://p.dw.com/p/3njeR
Kamerun Buea - Unruhen
Hoto: Getty Images/AFP/A. Huguet

Biyo bayan zafafa kai hare-haren kan mai uwa da wabi, mayakan 'yan aware da ke arewacin Kamaru a yankin masu amfani da Turancin Ingilishi na ci gaba da kutsawa yankin da ake amfani da harshen Faransanci.

Bayan da suka kai wani harin da ya hallaka sojojin Kamaru 4 da fararen hula 2, a wani gari mai suna Matazem da ke daf da iyakar yankin na ambazonia da yankin masu amfani da harshen na Farasanci. Ranar Larabar da ta gabata ma, mayakan sun kai farmaki a wani jerin gwanon motoci tare da halaka sojojin Kamarun hudu da farar hula daya.

Ministan yada labarai kuma mai magana da yawun gwamnatin kasar Rene Emmanuel Sadi ya bayyana cewa da alamu 'yan awaren sun mai da ayyukansu daf da yankin na masu magana da Faransanci.