Sabon sakon muryar Shugaban Boko Haram | Labarai | DW | 20.09.2015
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Sabon sakon muryar Shugaban Boko Haram

Shugaban Ƙungiyar Boko Haram Abubakar Shekau ya musanta duk wata nasara da rundunar sojojin Najeriya ke ikirarin samu a kan mayaƙansa

Shugaban Ƙungiyar Boko Haram Abubakar Shekau ya musanta duk wata nasara da rundunar sojojin Najeriya ke iƘirarin samu kan mayaƙansa da ma ƙoƙarin da gwamnatin Najeriya ke yi na neman canza tunanin ‘yan ƙungiyar. Ya bayyana haka ne a wani sabon saƙo na murya da reshen daular musulcin na yammacin Afirka ya fitar. Mutane da dama da suka saba sauraren saƙonnin Shekau ɗin a baya sun tabbatar da muryar ce a cikin sabon faifayin muryar.

Masharhanta sun bayyana cewar ƙungiyar ta fitar da wannan saƙo ne domin nuna cewa har yanzu har yanzu da ƙarfinta. Shugaban Ƙungiyar ta Boko Haram ya kuma jaddada goyon bayansu ga shugabaNnin Ƙungiyoyin gwagwarmaya kamar ISIS da Al-Qaida da saurann su.