Sabon rikici ya ɓarke a Gao dake arewacin Mali | Labarai | DW | 10.02.2013
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Sabon rikici ya ɓarke a Gao dake arewacin Mali

Dakarun ƙasar Mali sun yi arangama da ƙungiyar MUJAO masu kaifin kishin addini, a wannan karon, wani harin ƙunar baƙin wake ne ya yi sanadiyyar wannan gumurzu.

An yi wata taho mu gama a birnin Gao na ƙasar Mali tsakanin masu kaifin kishin addini da dakarun arewacin Mali, bayan da aka shafe kusan wuni biyu ana kai harin ƙunar baƙin wake a cewar wata majiyar soji.

Kamfanin dillancin Labarun DPA na Jamus ya rawaito cewa ƙaramin gungun 'yan tawayen na iya kasancewa 'yan MUJAO ne. Dakarun Mali da 'yan tawaye daga ƙungiyar ta MUJAO sun yi ta musayar wuta kan titunan cikin garin Gao kusa da shelkwatar 'yan sanda inda masu kaifin kishin addinin suka maida shelkwatar jami'an tsaronsu tsakanin watanni goman da suka riƙe arewacin ƙasar.

Wannan hargitsi ya sanya mutane gudu don tsira da rayuwarsu. Majiyan sojin ya ce wannan tarnaƙin ya yi mafari ne bayan da wani mai ƙunar baƙin wake ya jefa kansa a wani wurin binciken soji a daren Asabar.

Wannan harin dai ya nuna cewa barazanar bijirewar da 'yan tawayen suka yi zai zo gaskiya a yayinda Faransa wacce jiragen yaƙinta suka cigaba da luguden wuta a yankin arewacin Malin ke shirin janyewa daga ƙasar wata guda bayan ta shiga.

Mawallafiya: Pinaɗo Abdu Waba
Edita: Mohammad Nasiru Awal