Sabon rahoton kungiyoyi kan rikicin Siriya | Siyasa | DW | 12.03.2015
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Siyasa

Sabon rahoton kungiyoyi kan rikicin Siriya

Kungiyoyin kare hakkin jama'a da na agaji sun zargi kasashen duniya da zama sanadin halin da kasar Siriya ta samu kanta a ciki na tabarbarewar rayuwar fararen hula.

Rahoton wanda aka yi wa taken "Rashin nasara da gangan a Siriya" wanda hadin gwiwar kungiyoyin kare hakin jama'a da masu aiyukan jin kai su 21 suka wallafa, ya yi kakausar suka ga kasashen na duniya wadanda suka gaza amincewa da wasu kudurorin doka a karkashin Kwamitin Sulhu na Majalisar Dinkin Duniya domin daidaita al'amura a Siriya.

Inda a tsawon shekaru hudun da aka yi ana yakin basasa gwamnatin Bashar al Assad ta aikata ta'asa mafi muni a shekarar bara da ta wucce wato 2014, wanda a ciki mutane dubu 76 suka mutu, kana jumular wasu dubu 220 suka rasa rayukansu tun daga lokacin da aka fara tashin hankali na Siriya a shekarun 2011.

Ekkehard Forberg, na kungiyar agaji ta World Vision da ke a nan Jamus ya ce: "Dukkan kungiyoyin da suka wallafa wannan rahoton suna aikin agaji a Siriya saboda haka mun san abubuwan da ke wakana cikin kasar. A cikin shekarun 2013 da 2014 rikicin kasar ya kara yin muni, kana bukatar kayan jin kai ta karu yayin da kuma yawan wadanda aka tilasta musu barin yankunan na asali a cikin kasar ya karu matuka fiye da shekaru biyu na farkon rikicin."

Luftangriff des syrischen Regimes auf die Provinz Aleppo

Ayyukan ceto a rikicin Syriya

'

Kungiyoyin dai sun yi Allah wadai game da rashin katabus na kasashen duniyar da kuma kwamitin sulhu ya yi wajen ganin an cimma wani kudiri na musammun domin samar da masalha na wahalolin da farar hula suke gamuwa da su.

Kungiyon wadanda suka hada da Oxfarm da Save the Children da sauransu, sun zargi dukannin bangarorin biyu na gwamnatin da 'yan tawayen Siriya da kai hare hare a kan faran hula da gine ginen kasar wadanda suka hada da makarantu da asibitoci .

Majalisar Dinkin Duniya dai na bukatar kudade kusan biliyan takwas na dalar Amirka domin kawo dauki ga dubban fararen hula a Siriya. Sai dai har ya zuwa yanzu kashi 57 kawai cikin dari na kudaden aka samu.

Sauti da bidiyo akan labarin