Sabon ofishin yaƙi da Ebola a Afirka | Labarai | DW | 20.09.2014
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Sabon ofishin yaƙi da Ebola a Afirka

Za a girka ofishin ne domin ƙara azama bisa yaƙi da cutar ta Ebola, yanzu za'a kawo jami'an kula da lafiya kusa da ƙasashen da ke fama da cutar.

A cewar Majalisar Ɗinkin Duniya za ta buɗe ofishin yaƙi da cutar Ebola a yammacin Afirka wanda zai kasance a Accra babban binrin ƙasar Ghana, amma za su buɗe rassa a ƙasashen Laberiya, Saliyo da Gini. Sakatare janar na MDD Ban Ki-Moon, ya ce rashin fahimtar yanayin da ake kamuwa da cutar ya hana ɗaukar matakin daƙile annobar da yanzu ta hallaka mutane sama da 2600. Dubban jami'an kiwon lafiya a ƙasar Saliyo na ci gaba da binciken gida-gida domin zaƙulo waɗanda suka kamu da cutar ta Ebola.