Sabon nau'in Polio ya bulla a wasu sassan Najeriya
September 24, 2024Kasa da makonni biyu bayan da Najeriya ta sanar da sake bullar cutar shan Inna a kasar ne hukumar lafiya a matakin farko ta bayyana cewar kananan hukumomi 46 na jihohi 14 ne aka samu nau'i 14 na biyu na cutar, abin da ya nuna cewar aiki na neman komawa baya ga Najeriya. Idan za a iya tunawa, kasar ta yi gagarumin biki a 2020 na sallamar cutar Polio, amma bakon da aka yi sallama da shi bai yi nisa ba yanan nan labe.
Karin bayani: Najeriya: Shirin bankwana da Polio
Shugaban hukumar lafiya matakin farko ta Najeriyar Dr Muyiwa Aina ya ce wannan na nuna ci-gaba da yaduwar cutar Polio da ake samu, wanda dole ne a dauki mataki. Akwai matsaloli mabambanta da ake dangata su da dalilin sake bullar cutar Polio da ma yaduwarta a wadannan jihohi 14 da hukumar bata bayyana su ba saboda wasu dalilai.
A mafi yawancin jihohin arewacin Najeriyar, an fuskanci matsaloli na tashe-tahsne hankula musamman na ayyukan ta’adanci da masu ‘yan bindigar daji da suka katse hanzari na masu rigakafi a yankuna da dama. Babban aiki ne ke gaban hukumomii na ci gaba da wayar da kan jama’a a kan wannnan lamari.
Karin bayani: An kawar da Polio daga nahiyar Afirka
Hukumar lafiya a matakin farko ta sake farafdo da tarurruka da sarakunan gargajiya da shugabanin addinai a Najeriya, a kokarin sake shawo kan wannan matsalarPolio da ta sake kuno kai, inda a wannan karon ta gudanar da taro a karkashin inuwar cibiyar wanzar da zaman lafiya ta mai alkfarma Sarkin Musulmi Muhammad Sa’ad Abubakar, wanda ya bukaci hadin kai don yakar cutar. Ita ma hukumar lafiya a matakin farko ta bayyana cewa Najeriya na asarar yara kanana da ba su kai shekaru biyar da haihuwa ba har 2,300, abin da ke nuna rashin karuwar hanyoyin kula da lafiya musamman a yankunan karkara.