Sabon mummunan rikici a gabacin Ukraine | Labarai | DW | 03.06.2015
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Sabon mummunan rikici a gabacin Ukraine

Amirka ta nuna damuwa game da hare-haren 'yan awaren Rasha a gabacin Ukraine da cewa ba abin amincewa ba ne.

Ma'aikatar harkokin wajen Amirka ta ce gwamnatin kasar ta damu matuka game da rahotannin wasu hare-haren hadin guiwar da Rasha da kuma 'yan aware suka kai a gabacin Ukraine. Mai magana da yawun ma'aikatar harkokin waje Marie Harf ta ce ba za a amince da irin wadannan hare-hare ba da za su iya kaiwa a kara daukar matakan jan kunnen Rasha. A wannan Larabar dakarun Ukraine da 'yan aware magoya bayan Rasha sun yi gumurzu mafi muni cikin watanni. A wani labarin kuma fadar gwamnatin Kremlin ta zargi dakarun Ukraine da tsokanan fada a daidai lokacin da sabon rikici ya barke a gabashin kasar ta Ukraine. Sai dai gwamnati a birnin Kiev ta ce martani dakarunta suka kai bayan wani hari daga 'yan awaren.