1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Sabon kawancen tattalin arziki tsakanin tarayyar Turai da Afirka

Mohammad Nasiru AwalJune 1, 2006

Shirin zai yi adalci daidai wa daida tsakanin kasashen Turai da na Afirka.

https://p.dw.com/p/Btzt
´Yan kwadago a Afirka
´Yan kwadago a AfirkaHoto: DPA

A cikin kuduri game da nahiyar Afirka da ta zartas a cikin watan desamba, KTT ta tabo batun zaman lafiya da raya kasa a dangantaka tsakanin Turai da Afirka. Kungiyar EU ta ce zata fi ba da fifiko wajen taimakawa Afirka ta cimma burin nan na raya kasashe da ake yiwa lakabi da Millenium Goals kafin sherkara t a 2015. wasu muhimman batutuwan da kudurin ya kuntsa sun hada da tsaro da samar da shuganaci na gari.

Ko da yake Sven Grimm na cibiyar nazarin manufofin raya kasashe masu tasowa ta nan Jamus ya bayyana wannan matakin da cewa ba wani sabon abu ba ne amma ya ce a karon farko kungiyar EU mai membobi 25 ta gabatar da wani kundi mai kunshe da manufofin dabam dabam game da Afirka. 1. O-Ton Grimm:

“Da akwai wasu abubuwa da a da ma suke kunshe a manufarmu ta raya kasashe masu tasowa, alal misali kamar manufar kawantaka, amma ake fama da wahala wajen aiwatar da ita. Sabuwar manufar ketare, tsaro da huldar cinikaiya ma ta ambaci kalmar ta kawantaka. A saboda haka yanzu ya zama wajibi mu jira muga yadda zata kaya a tattaunawar cimma yarjeniyoyin ba juna hadin kai a fannin tattalin arziki.”

Yanzu haka dai kungiyar EU na tattaunawa da wasu kungiyoyin yankuna 4 na Afirka game da yarjeniyoyin, wadanda daga shekara ta 2008 zasu sake fasalta dangantakar tattalin arziki tsakanin Turai da Afirka, musamman akan yadda sassan biyu zasu kara bude kofofin kasuwanninsu ga kayayyaki daga nahiyoyin guda biyu.

Masu sukar wannan yarjejeniyar na fargabar cewa saboda karancin lokaci, Afirka ba zata samu damar cimma bukatunta a cikin yarjejeniyar ba. Amma a nata bangaren EU ta amince ta nuna adalci daidaiwa daida da Afirka. Wannan matsayin na EU na da nasaba da sabon kwarjinin dake tattare da kasashen Afirka.

Alal misali kungiyar tarayyar Afirka da kuma sabon kawancen raya kasashen Afirka wato NEPAD sun matsawa Turai lamba da ta canza salon tunanin ta a dangantakarta da wannan nahiya. Saboda haka yanzu an yi watsi da manufar nan ta gindaya sharudda ko yin barazanar janye taimakon raya kasa idan ba´a cike wadannan sharudda ba.

Majalisar Turai na goyon bayan sabon matsayin game da Afirka, inji wakiliyar NL Maria Martens. ´Yar majalisar ta ce aikin majalisar shi ne ta ba da fifiko tare da bawa Afirka damar fada a ji a dukkan matakan da za´a dauka da zummar cimma burin na Millenium Goals. Ita ma ta goyi da bayan cewa dole ne a nunawa Afirka adalci a cikin sabbin yarjeniyoyin hadin kan tattalin arzikin.

Kungiyoyin ba da taimakon raya kasa dake karkashi uwar kungiya mai suna VENRO a nan Jamus na ganin su ya kamata su sa ido wajen ganin an nuna wannan adalci. Shugabanta Bernd Pastors ya yi korafin cewa sabon shirin na EU game da Afirka bai tabo irin rawar da kungiyoyi masu zaman kansu zasu taka bisa manufa ba.

4. O-Ton Pastors:

“Ba´a bawa kungiyoyi masu zaman kansu damar ba da tasu gudunmmawa wajen tsara irin wadannan shirye shirye tun da farko. Ana tuntubar su ne kawai a matsayin ´yan cike gurbi. Wato abin nufi EU ba ta mu taimakon da muke bukata don gudanar da ayyukanmu tare da kawayenmu na Afirka.”

Ya zama wajibi shugabanni sun sa cewa hadin kai tsakanin kungiyoyin Turai da na kawayensu a Afirka na taimakawa wajen inganta zamantakewa tsakanin jama´a.