Sabon harin ta′addanci a Turkiya | Labarai | DW | 19.03.2016
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Sabon harin ta'addanci a Turkiya

Wani dan kunar bakin wake ya tashi bam a tsakiyar birnin Istanbul na kasar Turkiya inda ya hallaka mutane da dama.

Türkei Anschlag in Istanbul

Tsakiyar birnin Istanbul na kasar Turkiya inda aka Kai hari

Harin kunar bakin wake na birnin Istanbul da ya afku da safiyar wannan Asabar din an kai shi ne a wani babban titi da ake kira Istiklal da masu tafiya a kafa ke bi, inda ake da tarin manyan shagunan sayar da kayayyaki. Kawo yanzu dai an tabbatar da cewa harin ya yi sanadiyyar rasuwar mutane a kalla biyar tare da jikkata wasu mutane sama da 20 a cewar gwamnan birnin na istanbul. Wannan dai shi ne karo na biyu cikin watanni biyu da birnin na Istanbul ke fuskantar iri wannan hari na 'yan kunar bakin wake. Koda a ranar 12 ga watan Janairun da ya gabata ma dai wani dan kunar bakin waken ya tashi bam din da ke jikinsa a wurin da masu yawon buda ido 'yan kasashen waje suka fi halarta, harin da ya yi sanadiyar mutuwar mutane fiye da 10 akasarinsu 'yan kasar Jamus.