Sabon harin bom ya kashe mutane a Kano | Labarai | DW | 23.06.2014
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Sabon harin bom ya kashe mutane a Kano

Wani bom da ya fashe a kwalejin nazarin kiwon lafiya da ke jihar Kano a tarayyar Najeriya wato School of Hygiene ya yi sanadiyyar salwantar rayuka da dama.

Wannan bom dai ya tarwatse ne a tsakiyar kwalejin da misalin karfe biyu na ranar Litinin din nan 23 ga watan Yunin da muke ciki, inda ya hallaka mutane da kawo yanzu ba a tantance adadinsu ba. Wasu daliban kwalejin dake cikin yanayi na tashin hankali sun bayyana cewar suna tsaka da daukar darasi ne suka jiyo wata kara mai razanarwa a cikin makarantar wacce ta haddasa musu tsananin rudani.

Da yawa daga cikinsu dai sun bayyana cewar sun gano 'yan uwansu dalibai kwance cikin jini, yayin da wasu kuma da suka jikkata ke kukan neman agaji. Wakilinmu na Kano Nasir Salisu Zango ya ruwaito cewa ya zuwa yanzu jami'an tsaro sun tabbatar da faruwar lamarin sai dai komai ba a kan batun ba tukunna.

Mawallafi: Nasir Salisu Zango
Edita: Mouhamadou Awal Balarabe/LMJ