1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Hari ofishin 'yan sanda a Indonesiya

Yusuf Bala Nayaya
May 14, 2018

Wasu 'yan kunar bakin wake dauke da bam a ababen hawa sun tashi bam a hedikwatar 'yan sanda ta birnin Surabaya na kasar Indonesiya a wannan Litinin.

https://p.dw.com/p/2xf2H
Indonesien Präsident Joko Widodo am Ort des Bombenanschlags in Surabaya
Shugaba Joko Widodo ya je inda aka kai harin majami'ar a SurabayaHoto: Biro Pers Setpres

Mai magana da yawun 'yan sanda a gabashin Java Frans Barung Mangera ya ce fararen hula shida ne da 'yan sanda hudu harin ya raunata. Maharan hudu da 'yan sanda suka ce daga wani iyali ne guda sun halaka.

Wannan hari dai na zuwa ne kwana guda bayan wasu hare-hare tsararru guda uku a majami'u da suka halaka mutane takwas. Harin da jami'an 'yan sanda suka ce iyalai guda ne da suka hadar da yara 'yan mata tsakanin shekaru tara zuwa goma sha biyu suka kai harin na majami'a.