Sabon hari a Somaliya ya hallaka ′yan sanda | Labarai | DW | 18.10.2016
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Sabon hari a Somaliya ya hallaka 'yan sanda

Wata mota makare da bama-bamai da ta kutsa ofishin 'yan sanda a garin Afgoye a Somaliya ta yi sanadiyyar mutuwar jami'an 'yan sanda hudu.

Somalia Bombenanschlag in Mogadischu (picture-alliance/dpa/S. Y. Warsame)

Somaliya na ci gaba a fuskantar hare-haren ta'addanci

Wani babban jami'in dan sanda Nur Osman ya shaidawa kamfanin dillancin labarai na Reuters cewa mayakan tsagerun masu tarin yawa sun mamaye garin baki daya, yayin da ake ci gaba da yin bata kashi tsakaninsu da jami'an tsaro a garin na Afgoye, da ke da nisan kimanin kilomita 30 da Arewa maso Yammacin Mogadishu babban birnin kasar. Tuni dai mayakan kungiyar 'yan ta'addan al Shabaab da suka addabi kasar ta Somaliya suka dauki alhakin wannan hari. Kakakin kungiyar ta al shabaab Sheikh Abdiasis Abu Musab ya shaidawa kamfanin dillancin labarai na Reuters cewa a yanzu haka suna rike da yankuna masu yawa a kasar ta Somaliya.