Sabon Firamiyan Italiya, Romano Prodi, ya gabatar da manufofin gwamnatinsa ga Majalisa a birnin Rom. | Labarai | DW | 18.05.2006
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Sabon Firamiyan Italiya, Romano Prodi, ya gabatar da manufofin gwamnatinsa ga Majalisa a birnin Rom.

2. Sabon Firamiyan Italiya, Romano Prodi, ya gabatar da manufofin gwamnatinsa ga Majalisa a birnin Rom.

Romano Prodi, sabon Firamiyan Italiya da aka naɗa, ya yi wa Majalisar ƙasar jawabi a karo na farko yau a birnin Rom, inda ya bayyana muhimman manufofin da gwamnatinsa ta sanya a gaba. Ɗaya daga cikin waɗannan manufofin kuwa, ta shafi batun janye dakarun Italiyan kusan su dubu 3 ne daga Iraqi cikin gaggawa. Firamiyan ya ce, wannan shi ne farkon matakin da zai ɗauka, amma sai bayan ya yi shawarwari da abokan burmin Italiyan. Game da afka wa Iraqin da yaƙi dai, Romano Prodi, ya bayyana cewa:-

„Yaƙan Iraqin, da kuma mamaye ta da aka yi da dakaru, wani babban kuskure ne a namu ganin. Ba ta hakan ne za a iya shawo kan matsalolin tsaro ba. A daura da haka ma, sai dai a ƙara taɓarɓare al’amura. Yanzu haka, aƙidar ta’addanci ta sami wani sabon tushe a Iraqin. Wannan gwamnatin na shirin gabatar wa majalisa shawarar janye sojojinmu daga ƙasar.“

Game da harkokin cikin gida kuma, Romano Prodi, ya ce ana bukatar ɗaukan tsauraran matakai, don magance komaɗar tattalin arzikin da Italiyan ke huskanta.