Sabon firaminstan Mali na shirin girka gwamnati | Labarai | DW | 06.09.2013
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Sabon firaminstan Mali na shirin girka gwamnati

Bayan da ta shafe watanni 18 tana fama da rikici 'yan ƙasa sun fara shirin ganin yadda za a aiwatar da alƙawuran sabon shugaban ƙasa IBK na samar da haɗin kan 'yan ƙasa

Former Malian Prime minister Django Sissoko (R) shakes hands with newly appointed Prime minister Oumar Tatam (L) during the handover ceremony, on September 6, 2013 in Bamako. Oumar Tatam Ly, appointed as Mali's first post-conflict prime minister on September 5, 2013, has impressed observers as a high-flying banker with more than two decades' experience in international finance.AFP PHOTO HABIBOU KOUYATE (Photo credit should read HABIBOU KOUYATE/AFP/Getty Images)

Sabon Firaminista Oumar Tatam Ly

Firaministan Mali na farko bayan rikicin da ya ɗaiɗaita ƙasar ya fara ƙoƙarin girka gwamnatin da ake sa ran zai aiwatar da alƙawuran da sabon shugaban ƙasa Ibrahim Boubacar Keita ya yi na haɗa kan 'yan ƙasa da kuma yaƙi da cin hanci da rashawa.

Sabon shugaban ƙasar Mali Ibrahim Boubacar Keita ya zaɓi ƙwararraren ma'aikacin bankin nan mai suna Oumar Tatam Ly a matsayin firaminista, mai shekaru 49 na haihuwa wanda ya kasance mashawarcin gwamnan babban bankin yammacin Afirka wato Central Bank of West Africa ko kuma BCEAO wanda ke Dakar babban birnin Senegal, ya bayyana cewa a shirye ya ke ya tinkari duk wani ƙalubale da ma ayyukan da shugaban ƙasa ya ba shi.

Yanzu dai Ly ya gurbin Diango Cissoko wani tsohon ma'aikacin gwamnati wanda ke riƙe da muƙamin a gwamnatin riƙon da aka kafa a watan Disemban shekarar 2012.

M. Oumar Tatam Ly na shawarwarin girka gwamnatin da za ta jagoranci ƙasar wadda al'ummarta ke da yawan milliyan 16.

Mawallafi: Pinaɗo Abdu Waba
Edita: Umaru Aliyu