Sabon firaministan Yemen ya yi marabus | Labarai | DW | 09.10.2014
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Sabon firaministan Yemen ya yi marabus

Ahmed Awad Ben Mubarak ya ce ya ajiye aikin ne domin samun haɗin kan ƙasar.

Marabus ɗin na firaminista na da nasaba ne da ƙin amncewa da 'yan tawayen na 'yan Shi'a waɗanda ke da iko da birnin Sana'a tun cikin watan Satumba suka ƙi amincewa da naɗin.

A cikin wata wasiƙa da ya aikewa shugaba Abd Rabo Mansur Hadi,firaminista ya ce ya ɗauki wannan mataki ne domin kaucewar rabuwar kasar gida biyu. A cikin watan jiya ne aka cimma wata yarjejeniya dakatar da buɗe wuta tsakanin gwamnatin da 'yan tawayen a ƙarƙashin jagorancin Majalisar Ɗinkin Duniya tare da kafa gwamatin haɗin kansa.