Sabon fada tsakanin sojin gwamnati da ´yan tawaye a Sri Lanka | Labarai | DW | 30.09.2006
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Sabon fada tsakanin sojin gwamnati da ´yan tawaye a Sri Lanka

´Yan sanda a Sri Lanka sun ce sun halaka ´yan tawayen kungiyar Tamil Tigers akalla 12, wadanda suka kai hari akan wani sansanin ´yan sanda a Pullumalai dake gundumar Ampara a gabashin wannan tsibiri. Kawo yanzu ´yan tawayen ba su tabbatar da wannan labari ba. A kuma halin da ake ciki rundunar sojin kasar ta ce an kashe ´yan sanda 3 a wani harin bam da aka kai a gundumar Mannar. Fadan wanda ya yi muni tun bayan kulla wata yarjejeniyar dakatar da yaki a shekara ta 2002, ya zo ne gabanin ziyarar da mai shiga tsakani na kasar Norway wato Jon Hanssen-Bauer zai kaiwa kasar a ranar litinin.