Sabon fada a gabashin Ukraine | Labarai | DW | 03.10.2014
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Sabon fada a gabashin Ukraine

Dakarun gwamnatin Ukraine sun gwabza fada da 'yan aware a gabashin kasar a yunkurin da suke na karbe iko da wani filin jirgin sama da ke arewacin birnin Donetsk.

'Yan awaren dai sun sanar da cewar su ne ke rike da filin jirgin saman bayan da suka fattattaki sojin gwamnatin kasar da suka karbe wajen na wani dan lokaci.

Kaurewar wannan sabon fada na zuwa ne a daidai lokacin da gwmanatin Ukraine din da 'yan aware ke zargin juna da kisan wani ma'aikacin bada agajin gaggawa dan asalin kasar Switzerland.