Sabbin tashe tashen hankula a birnin Bagadaza | Labarai | DW | 16.06.2006
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Sabbin tashe tashen hankula a birnin Bagadaza

Kwanaki biyu kadai bayan da dakarun kasa da kasa da kuma na Iraqi sun kaddamar da wani gagarumin matakan tsaro a birnin Bagadaza, wani dan kunar bakin wake ya halaka akalla mutane 11 sannan ya jiwa 25 rauni a wani hari da ya kai kan wani masallacin ´yan shi´a. An kai wannan harin ne a daidai lokacin da masu ibada suka taru don yin sallar juma´a a masallacin Buratha. Jim kadan bayan wannan hari ´yan sanda sun ce wata roka ta afkawa wata unguwa dake wajen birnin na Bagadaza inda ta halaka akalla mutane 3 sannan 16 suka jikata.