Sabbin takunkumi kan Rasha sun fara aiki | Labarai | DW | 12.09.2014
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Sabbin takunkumi kan Rasha sun fara aiki

A wannan Juma'ar ce sabbin takunkumin da kungiyar tarayyar Turai da Amirka suka kakabawa Rasha kan hannun da suka ce tana da shi a rikicin gabashin Ukraine ke fara aiki.

To sai dai a daura da hakan, fadar mulkin Rasha ta Kremlin ta nuna rashin amincewarta yayin da ma'aikatar harkokin wajen kasar ta ce daukar wannan mataki ya nuna cewar EU da Amirka sun kawar da kansu daga yunkurin Rasha na ganin an sasanta rikicin Ukraine din cikin ruwan sanyi kuma ba za su yi kasa a gwaiwa ba wajen maida martani.

Wannan dai na zuwa ne daidai lokacin da gwamnatin Ukraine da kungiyar tsaro ta NATO suka bada labarin cewar sun tsinkayi sojin Rasha kimanin dubu guda a wani yunkuri da suka ce na agazawa ne 'yan awaren da ke gabashin Ukraine din.

Mawallafi: Ahmed Salisu
Edita: Usman Shehu Usman