1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Sabbin sauye-sauyen Paparoma Francis

July 11, 2013

A wani mataki na yaƙi da cin zarafin ƙananan yara a Vatican, Paparoma Francis ya ƙarfafa dokar ta za ta hukunta duk wanda aka kama da laifi yadda ya kamata

https://p.dw.com/p/196Lc
Pope Francis prays as he leads the weekly audience in Saint Peter's Square at the Vatican June 12, 2013. REUTERS/Tony Gentile (VATICAN - Tags: RELIGION)
Hoto: Reuters

Paparoma Francis ya ƙara ƙarfafa sabuwar dokar da ta haramta cin zarafin ƙananan yara a Vatican, ya kuma ɗauki matakan da suka ƙarawa ma'aikatan fadar nasa alhakin sanya ido dan kama masu laifi yadda ya kamata.

A wata sanarwar da fadar ta Vatican ta fitar, dokar Paparoman ya ƙara faɗaɗa bayanai dangane da hujjojin da za a yi la'akari da su wajen tantance laifukan da za a kira cin zarafin ƙananan yara.

Waɗannan dokoki dai na daga cikin matakan da mahukuntan na Vatican suka ɗauka na yin la'akari da ire-iren laifukan da ƙududrin ƙasa da ƙasa ya tanada, domin kwaskware dokokinsu na cikin gida, kasancewar ita kanta Vatican ta sanya hannu kan wannan ƙuduri. Dokokin da aka gyara sun shafi laifukan da suka haɗa da nuna wariyar launin fata, manyan laifukan yaƙi da cin zarafin ƙananan yara.

Paparoma Francis ya kuma ƙara inganta dangantakar dake tsakanin fadar tasa da sauran ƙasashe domin kama masu halatta harmtattun kuɗaɗe da ta'addanci, a wani mataki na tabbatar da ɗorewar sauye-sauyen da magabacinsa Paparoma Benedict na 16 ya aiwatar.

Mawallafiya: Pinaɗo Abdu Waba
Edita: Mohammad Nasiru Awal