Sabbin sauye-sauye a Iraki | Labarai | DW | 11.08.2015
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Sabbin sauye-sauye a Iraki

'Yan majalisar ƙasar Iraƙi sun amince da sauye-sauyen da suka haɗa da guraben muƙaman gwamnati da kuma yunƙurin kawo ƙarshen rashin jituwar ƙabilun ƙasar.

'Yan majalisar dokokin ƙasar Iraki sun kaɗa ƙuri´a da mafi rinjaye domin amincewa da jadawalin sauyin da firaministan ƙasar Haider Al Abadi ya gabatar musu.Kakakin majalisar asar Saleem Al Jabouri shi ne ya bayyana hakan a yayin zaman zauran majalisar a ranar talatar nan da aka yaɗa a kafafen watsa labaran ƙasar.

Shugaba Abadi ya ɓullo da wasu matakai ne domin daƙile mattsalolin da suka shafi cin hanci da rashawa tare da adana kuɗaɗe don ci gaban ƙasar. Matakan dai sun ƙunshi soke manyan guraben muƙamai a gwamnatin ƙasar tare da kawo ƙarshen rashin jituwar ƙabilu gami da sake buɗe wani sabon babin binciken cin hanci da rasha a ƙasar baki ɗaya.