1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Sabbin ministocin gwamnatin Jamus

CDU, SPD, Merkel, JamusDecember 16, 2013

Shugabar gwamnatin Jamus Angela Merkel ta bayyana sunayen ministocin da za su yi aiki da ita a wa'adinta na uku musamman ma dai wanda suka fito daga jam'iyyarta ta CDU.

https://p.dw.com/p/1Aa9t
Hoto: picture-alliance/dpa

Shugabar gwamnatin Jamus Angela Merkel ta gudanar wani taron manema labarai a birnin Berlin jiya da yamma inda ta ce jam'iyyarta za ta ci-gaba da rike mukaman da suka hada da na ministan tsaro da na harkokin kudi da na harkokin cikin gida. An dai nada Ursula von der Leyen a mastayin mace ta farko da za ta jagoranci harkokin tsaron kasar.

Ita ma jam'iyyar SPD da ke kawance da ta Merkel din ta bayyana mukamai na ministoci shidda da ta samu wadda suka hada da ministan harkokin waje da na kwadago da kuma ministan tattalin arziki da makamashi.

Tuni dai masu fashin bakin siyasa a kasar suke cewar yadda aka yi rabon mukaman a gwamnatin hadin gwiwar musamman ma dai masu maiko ya nuna cewar Angela Merkel na rike da ragamar gwamnatin fiye da yadda aka yi tsammani.

Mawallafi: Ahmed Salisu
Edita: Mouhamadou Awal Balarabe