Sabbin hare-haren bama-bamai a Najeriya | Siyasa | DW | 18.11.2015
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Siyasa

Sabbin hare-haren bama-bamai a Najeriya

Ana kyautata zaton mutane da yawa sun mutu a tagwayen hare-haren da aka kai a Kano kwana guda bayan harin Yola inda mutane kimanin 34 suka mutu wasu akalla 80 suka jikkata

Harin na Kano dai ya faru ne a Kasuwar wayar hannu ta Farm Center, abin da kuma jawo mutuwar mutane kasance wa an kai harin ne lokacin da mutane ke kai kawo. Jami'an ceto na ci-gaba da tantance iya wadanda lamarin ya shafa.

A harin birnin Yola na jiya Talata kuwa, shaidun ganin ido sun shaidar cewa wani mutum ne ya zo cikin mutane yana raba musu kudi, kwatsam sai wani abu ya fashe. Ana kuma kyautata zaton cewa bam din a jikinsa yake a daure kuma ya tashi da shi. Ko da yake harin na Yola shi ne harin farko da ya auku a cikin wannan wata, abinda ke nuna alamar cewa sabbin dabarun yaki da sojojin Najeriya suka dauka yana samun nasara, amma fa batun kawo karshen tarzomar Boko Haram a karshen watan gobe, abu ne da ke da wuya.

Harin dai ya zo ne kwanaki kadan bayan da shugaba Muhammadu Buhari ya kai ziyara a birnin Yola, inda ya gana da wasu daga cikin sojojin da suka jikkata sakamakon yaki da Boko Haram.

A martaninsa kan harin Shugaba Buhari ya jajantawa iyalan wadanda suka rasu a harin, kana ya yi addua'ar Allah ya bai wa wadanda suka jikkata lafiya. Buhari ya jaddada aniyarsa ta murkushe 'yan ta'addan kungiyar Boko Haram., yana mai cewa, "Makiyanmu ba za su taba yin nasara ba. Za mu hada karfi da karfe domin murkushe ta'addanci".

Shi ma dai shafin sada zumunta na zamani wato Facebook, ya bude wani bangare na musamman a Najeriya domin bai wa mutane damar binciken bayanai ta Facebook don tsare kansu, inda aka fidda shafin bayan harin da ya faru a Yola babban birnin jihar ta Adamawa. Al'umar jihar Adamawa dake arewa maso gabashin Najeriya sun yi marhabin da samun wannnan dandali da shafin facebook ya samar don musayar bayanai a wuraren da ke fama da rikice-rikice, a wani kokari na amfani da fasahar wajen ceto jama'a.

Samun dandalin sada zumunta a shafin facebook wato Safety Check karon farko a Najeriya ci gaba ne da fasahar zamani ta kawo, inda zai hada al'umma wajen musayar bayanai na fadakar da juna musamman a wuraren da ake samun tashe-tashen hankula, don gujewa fadawa cikin hatsari.

Akasarin masu amfani da shafin facebook tsakanin jama'a musamman matasa da suka fi amfani da intanet, dama manya cikin rukunin jama'a saboda hakan ne ma aka soma marhabin da wannan fasaha da zamani ya kawo, wanda tuni mutane a Yola suka nuna shirin su na shiga wannan dandalin na ''Safety Check'' don samar da bayanai a wannan bangare na Najeriya.

Sauti da bidiyo akan labarin