Sabbin hare-hare sun hallaka mutane da dama a Iraƙi | Labarai | DW | 24.04.2013
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Sabbin hare-hare sun hallaka mutane da dama a Iraƙi

Waɗannan hare-hare su ne mafi muni a hare-haren da ake dangantawa da zanga-zangar 'yan sunni, waɗanda ke nuna adawa da gwamnati, wacce su ke zargi tana ƙuntata musu.

Tahse-tashen hankula sun kai ga hallakar wasu mutane 15 waɗanda a ciki 14 jami'an tsaro ne da 'yan bindiga, a misayar wutar da ya afku tsakaninsu, a cewar hukumomi.

Artabu tsakanin tsakanin jami'an tsaro da masu zanga-zanga kusa da garin Hawijah ya hallaka mutane 27 tun a ranar talata abun da ya janyo ramuwar gayyar da ta ƙara hallaka wasu 27.

Wannan kisan ramuwar gayyar ce ake cigaba da yi har a yau laraba inda kawo yanzu jami'an tsaro tara da 'yan bindiga uku sun hallaka. Masu zanga-zanga a yankunan da 'yan Sunni ke da rinjaye sun ɗauki watanni hudu suna gudanar da jerin gwano suna kuma kira ga shugaban ƙasa Nuri al-maliki da yayi murabus suna kuma yin Allah Wadai da zargin cewa hukumomin, waɗanda mafi rinjaye 'yan shi'a ne na muzgunawa tsirarun al'ummomin 'yan sunni.

Kawo yanzu dai, waɗannan hare-haren da aka fara ranar talata shine mafi muni a cikin waɗanda ake dangantawa da zanga-zangar ta 'yan Sunni.

Mawallafiya: Pinaɗo Abdu Waba
Edita: Usman Shehu Usman