Sabbin hare-hare a Syria | Labarai | DW | 19.02.2018
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Sabbin hare-hare a Syria

Wasu jiragen yakin gwamnatin kasar sun yi luguden wuta a gabashin Ghouta, bayan samun bayanan yiwuwar fuskantar artabu daga mayakan tawaye da ke a yankin.

Rahotannin dake fitowa daga Syria, na cewa wasu jiragen yakin gwamnatin kasar sun yi luguden wuta a gabashin Ghouta, bayan samun bayanan yiwuwar fuskantar artabu daga mayakan tawaye da ke a yankin. Gabashin na Ghouta wanda yanki ne na karshe da ya saura a hannun 'yan tawaye a kewayen birnin Damascus, na fuskantar fushin gwamnatin shugaba Bashar al-Assad, bayan aikewa da wasu zaratan dakaru 'yan hadarin safe maganin uba mai tsanani.

Ko a farkon wannan watan ma dai, sai da mayakan gwamnati suka dauki kwanaki biyar cur suna ruwan boma-bomai, inda shaidu suka ce akalla fararen hula 250 sun salwanta, wasu daruruwan kuma suka ji jiki.