Sabbin hanyoyi na yaki da talauci | Jigo | DW | 12.09.2013
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Jigo

Sabbin hanyoyi na yaki da talauci

Ko da shike batun agaji, ba ya taka rawa a gangamin yakin neman zaben Jamus, amma galibin Jamusawa na goyon bayan karin agaji ga ketare.

Sakamakon kuri'ar jin ra'ayin jama'a dai ya nunar da cewar, kaso 80 cikin 100 na jamusawa ne ke goyon bayan karin tallafi ga sha'anin raya kasashe.

Bayan darewa mukamin ministan raya kasashe na Jamus a shekara ta 2009, Dirk Niebel, dan jam'iyyar Free Democrat, ya nuna bajinta wajen aiwatar da manufofin ma'aikatar, inda aka samu ci gaban da ya zarta wanda aka gani cikin shekaru 20 da suka gabata.

Ya rungumi tsarin da a karkashinsa, Jamus ba wai ta kasance babbar mai bada agaji domin raya kasashe kadai ba, a'a harma da samun kudin shiga daga agaji. A bisa wannan manufar dai, gwamnati na zama babbar mai samar da kudaden tafiyar da ayyuka, amma kuma tana marhabin da kamfanoni masu zaman kansu a matsayin abokan aiki wajen ci gaba, domin abin da minista Dirk Niebel ya ce amfanar dukkan bangarori:

Ya ce " Darasin da na koya cikin shekaru hudun da suka gabata, shi ne cewar, bangaren 'yan kasuwa masu zaman kansu da sauran masu taka rawa a fannin tattalin arziki, za su iya yin aiki kafada da kafada. Hatta kungiyoyin da a baya ba sa cudanya da 'yan kasuwa, sun gano cewar, tattalin arziki zai taimaka musu wajen samar da kudaden cimma muradunsu. Kungiyoyin farar hula za su iya bayar da gudummowar kwararrun da suke dashi ta hanyar sanya al'umma cikin ayyuka da kuma nagartar aikin kansa, har kuma ya zuwa tsara sha'anin kasuwanci a lokaci guda. Sakamakon kan zama mai ban sha'awa inda kowa ke amfana."

ARCHIV: Entwicklungshilfeminister Dirk Niebel (FDP) posiert in Faisabad in Afghanistan mit seiner Gebirgsjaegermuetze aus seiner Zeit bei der Bundeswehr (Foto vom 30.03.11). Die Bundeskanzlerin geht davon aus, dass Entwicklungsminister Dirk Niebel seine Versaeumnisse in der Teppich-Affaere rasch bereinigt. Merkel sei sicher, dass die Verzollung des privat erworbenen Souvenirs aus Afghanistan so schnell und so vollstaendig wie moeglich nachgeholt wird, sagte ein Regierungssprecher am Freitag (08.06.12) in Berlin. Der FDP-Politiker hatte das Souvenir im Mai im Dienstjet des BND-Chefs von Kabul aus nach Deutschland mitnehmen lassen, da er mit einer Linienmaschine angereist war und den sperrigen Teppich nicht mitnehmen konnte. Fuer den Transport zahlte der Minister keine Gebuehren. Auch wurde dem deutschen Zoll die Ware nicht vorgelegt. (zu dapd-Text) Foto: Sascha Schuermann/dapd

Ministan raya kasashe na Jamus, Dirk Niebel

Kawance tsakanin 'yan kasuwa da hukumomi ne tushen ci-gaba

Wannan tsarin da ministan raya kasashen ke bi dai, ya sami yabo daga shugabar gwamnatin Jamus Angela Merkel, da kuma shi kansa shugaban bankin duniya, Jim Yong Kim, wanda ma yayi tsokaci a kai :

Ya ce " A ra'ayina muhimmin batu ba wai na ko mutum yana nuna goyon baya ko kuma adawa da bangaren 'yan kasuwa masu zaman kansu ba ne. Muhimmiyar tambaya, ita ce yaya manufarka take a kokarin biyan bukatun mutanen da suka fi fama da talauci? Domin kuwa idan kana da kyakkyawar manufa, to, kuwa za ka yi kokarin ganin kowace dala daya ka bayar a matsayin agaji, zai iya janyo samar da wasu kudade. Domin ba za mu taba cimma muradunmu ba, kuma ba za mu taba iya fidda jama'a daga kangin talaucin da suke fama dashi a ko ina cikin fadin duniya ba, har sai mun samar da yanayin da kanfanoni da hukumomin gwamnati za su kulla kawance da 'yan kasuwa masu kansu."

ARCHIV - Der Präsident des Dartmouth College, Jim Yong Kim, lächelt am 23.03.2012 im Garten des Weißen Hauses in Washington, USA. US-Präsident Obama will Jim Yong Kim als neuen Weltbankchef - und nach alter Tradition ist sein Wunsch Befehl. Doch erstmals gibt es heftigen Widerstand gegen den US-Kandidaten. Foto: EPA/ANDREW HARRER/POOL (Zu dpa «Tradition oder Revolution? Weltbank bestimmt neuen Präsidenten» vom 15.04.2012) +++(c) dpa - Bildfunk+++

Shugaban bankin duniya, Jim Yong Kim

Abubuwan da ke kawo cikas ga bunkasar kasashe matalauta

Fannin da ministan raya kasashe na Jamus Dirk Niebel ke ganin zuba kudi a ciki zai taimakawa ci gaban tattalin arziki da saukaka talauci kuwa, shi ne na samar da ababen more rayuwa, da suka hada da Ilimi, da kiwon lafiya, sai kuma ruwan sha da makamashi.

Sai dai duk da rawar da Jamus ke takawa a fannin agaji, wasu na sukarta, saboda hatta a bara, yawan kajin da take safararsu zuwa Afirka ya karu da fiye da kaso 120 cikin 100, abin da kuma ke yin kafar ungulu ga masu sana'ar kiwon kaji a nahiyar. Bugu da kari kuma, tallafin da kasashen da suka ci gaba ke baiwa manomansu, na hana manoman kasashe masu tasowa samun amfani sosai a kasuwannin duniya, lamuran da ko da shike Niebel ya yi na'am dasu,, amma kuma babu wata alamar yin gyara a aikace.

Mawallafi : Fürstenau, Marcel / Saleh Umar Saleh
Edita : Umaru Aliyu

Sauti da bidiyo akan labarin