Sabbin dokokin tuƙi a Nijar | Siyasa | DW | 14.12.2012
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Siyasa

Sabbin dokokin tuƙi a Nijar

A ƙoƙarin rage yawan haɗaruruka bisa tituna gwamnatin Jamhuriyar Nijar ta tsaurara dokokin tuƙi.

Gebäude des Parlaments der Republik Niger, Niamey. Foto: Mahaman Kanta/DW, 19.5.2011, Niamey / Niger, Zulieferer: Thomas Mösch

Majalisar Dokokin Nijar

A Jamhuriyar Nijar gwamnatin ƙasar ta bada sanarwar fito da
wani sabon kundin dokokin tuƙi a wani mataki na rage yawan
haɗurran ababan hawa da ake fuskanta.Dokar dai ta tanadi
sauyi a cikin tsarin bayar da lasin izinin tuƙin mota da
yawan shekarun motocin da za dinga shigo da su a ƙasar daga waje da dai sauran matakai daban-daban.Taron Majalissar ministocin ƙasar ya baiyana ɗaukar wannan sabon mataki.

Wannan dai shine karo na farko tun bayan shekarar 1963 wato shekaru ukku bayan samun yancin kan ƙasar da gwamnati ke sake kundin dokokin tuƙi a Nijar. Gwamnati ƙasar ta bayyana
cewa na farko dai ta ɗauki matakin, domin magance matsalar yawan
haɗurran da ake fuskanta a ko wace shekara. Irahim
Yakuba, ministan ma'aikatar suhuri ta ƙasa ya yi ƙarin bayani kan
wananan matsala:
Wani rahoto na Hukumar Lafiya ta Duniya wato OMS ko WHO,na shekara ta 2009 ya bayyan ƙasar a matsayin wace ta fi ko wace ƙasa yawan haɗurran kan hanya, daga cikin jerin ƙasashen Afrika ta Yamma, inda ta ce daga cikin mutane dubu ɗari na Nijar, kimanin 38 na mutuwa ne sanadiyyar haɗarin kan hanya.To saidai gwamnatin ta ce ta gano cewa waɗannan haɗurra su da kansu na wakana sabili da wasu matsaloli da su ke da nasaba da rauni da dokokin tuƙin na yanzu su ke da.
Wannan sabon kundin dokokin tuƙi da gwamnatin ƙasar ta fito da
shi dai ya tanadi sauye-sauye a fannonin daban-daban da gwamnatin ta ce za su taimaka ga rage kaifin matsalar ƙaurin suna da ƙasar ta yi wajan yawan haɗurra kan hanyar. Ibrahim Yakuba ministan suhuri na

Nijar ya zano wasu daga cikin tanade-tanaden da wannan sabon
kundin dokokin tukin ya ƙunsa:
Dama dai a baya a ƙoƙarin da ta ke na magance wannan matsala,
gwamnatin Nijar ta farfaɗo da dokar saka hullar kwano ga masu
babura da ma dokar da ta hana ɗaukar salula a cikin tuƙi;A nan gaba
dai gwamnatin ƙasar za ta shigar da wannan baƙuwar dokar tuƙin a
gaban Majalissar Dokoki domin neman amincewarta da ita.

Mawallafi: Gazali Abdou Tasawa
Edita: Yahouza Sadissou Madobi

Sauti da bidiyo akan labarin