Sabbin dabarun kere-kere a Baswana | Himma dai Matasa | DW | 07.06.2017
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Himma dai Matasa

Sabbin dabarun kere-kere a Baswana

Sabuwar na'urar matsar gyada gami da sabbin dabarun kere-kere sun tamaka ga bunkasa rayuwar mutane a wani yankin na kasar Baswana mai fama da talauci.

Na'urar dake saukaka aikin tatsar man gyada zuwa sabon basirar kera kekunan guragu da ka iya gudu koda a cikin rerayi da kuma injin wankin kaya da baya bukatar ruwa mai yawa don wanke-wanke,. Kadan kenan daga cikin na'urorin da al'ummar kauyen San ke anfani da fasahar zamani don sarrafa kayyakinsu na gargajiya  don bunkasa sana'oi da zai bai wa al'umma damar dogaro da kai maimakon jiran gwamnatin dake fama da matsala a tattalin arziki.

A yankin Kalahari da ke tsakiyar kasar Botswana, al'ummar garin San mutane ne da ke matukar alfahari da al'adarsu ta gargajiya da kuma irin basirar da suke da ita wajen gudanar da ayyukansu na yau da kullum, al'ummar yankin dai na fama da tsanani na rayuwa idan aka duba yadda suke rayuwa ta hanyar amfani da karfi wajen sarrafa anfanin gona zuwa sauran abubuwan bukatun yau da kullum. Yanzu dai za a iya cewa an sami ci gaba tun bayan da wata kungiya mai zaman kanta ta bijiro da shirin fahintar da al'umma fa'idar sarrafa kayayakinsu na gargajiya ta hanyar anfani da fasahar zamani a wani mataki na inganta rayuwarsu.

Dan asalin Botswana Thabiso Mashaba dai ya hada kai da shugabanin kauyukan da kuma masu ilimin fasahar kere-kere na zamani daga kasashen Amirka don samar da shirin da zai fahintar da jama'a kan koyar sana'a ta hanyar amfani da na'urorin da aka kirkira ta fasahar zamani daga kayyakin gargajiya da ke a wannan yankin.

Al'ummar garin  San sun dadde suna rayuwa cikin tsanani sanadiyar halin da tattalin arzikin kasar ke fuskanta, har yanzu dai al'umma na ci gaba da fuskantar matsaloli na rashin aikin yi da kuma talauci matasa ba su da zabi face su bar kasar.

Thabiso Mashaba dai na ganin al'ummar yankin na da rawar da za su taka na samar da ci gaba a yankin ta fannin sarrafa nasu kayan gargajiya da fasahar zamani duk da matsanancin talauci da aka san yankin da shi.

Wata kungiya mai zaman kanta da ke Amirka da ake kira ‘International Development Innovation Network‘ karkashin jagorancin Thabiso Mashaba ta yi kokari wajen ganin ta kafa wata kungiya a kauyen D'kar inda ake horas matasa da ke da basira kan fasahar kere-kere da zane da zummar samar da kananan sana'oi da za su iya dogaro da kansu.