Sabanin ra′ayi tsakanin shugabannin Turai dangane da makomar ′yan gudun hijira | Siyasa | DW | 03.09.2015
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Siyasa

Sabanin ra'ayi tsakanin shugabannin Turai dangane da makomar 'yan gudun hijira

Kasar Hangari ta nemi girmama dokokin kasashen Turai kan baki 'yan gudun hijira inda ta bukaci su yi rigista kamar yadda tsarin ya tanada.

Yayin da dubban 'yan gudun hijira daga kasashen da ke fama da rikice-rikice a Gabas ta Tsakiya, wasu daga Afirka suka isa birnin Munich Jihar Bavaria da ke kudancin Jamus inda suka samu tarba ta al'ummar yankin, 'yan uwansu dubbai da suka makale a tashar jirgin kasa a Budapest a kasar Hangari na ci gaba da kira da a kawo musu dauki.

Cikin wadannan 'yan gudun hijira kimanin 3500 sun sauka ne a tashar jirgin kasa da ke a Munich a nan Jamus inda suka sami tarba ta musamman ga al'ummar wannan yanki wadanda ke dauke da kwalaye da rubutu wanda ke cewa " 'yan gudun hijira muna muku lalale marhabun."

Fa'iz Ahmad dan kasar Pakistan na daga cikin 'yan gudun hijira da suka isa birnin na Munich. Kuma ya nuna godiya sakamakon isa kasar ta Jamus.

Mahukunta a wannan kasa dai sun bayyana cewa suna yin duk mai yiwuwa wajen ganin sun tallafa wa mutane da suka samu kansu cikin hali na tsananin bukata. Shi kuwa Thomas Duchmann cikin Jamusawa da suka sadaukar da lokacinsu suna aikin jinkai ga wadannan dubban 'yan gudun hijira, ya ce za su ci gaba da wannan sadaukarwa har sai mahukunta sun karbi wannan aiki.

Baya ga wadanda suka isa Jamus wasu 'yan gudun hijirar sun tsinci kai cikin hali na tsaka mai wuya bayan da 'yan sanda a Hungary suka hana musu damar ketara iyaka zuwa Ostriya daga nan su je Jamus, wata kwarya-kwaryar zanga-zanga suka yi bayan kwana a filin Allah gaban tashar jirgin kasa ta Keleti a Budapest fadar gwamnatin kasar Hangari inda suka ce su fa zaman lafiya suke muradi.

Wani dan fafutukar kare hakkin dan Adam a kasar ta Hangari da ya bayyana kansa da suna dan fafutika Gabor ya ce kasashen na Turai nada yadda zasu yi su tallafi wadannan mutane da ke cikin halin kunci.

Ita kuwa uwargida Meshde da ta fito tare da 'ya'yanta daga yankin Aleppo na kasar Siriya cewa tayi a bata dama ta bar kasar ta Hungary kamar sauran 'yan uwanta da suka siyi tikitin jirgin kasa amma aka hanasu ficewa.

DW.COM

Sauti da bidiyo akan labarin