Sabanin ra′ayi kan juyin mulkin Lesotho | Siyasa | DW | 02.09.2014
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Siyasa

Sabanin ra'ayi kan juyin mulkin Lesotho

'Yan siyasa da al'ummar kasar Lesotho gami da masu fashin baki na harkokin mulki da na siyasa na cigaba da bayyana mabanbanta ra'ayoyi kan juyin mulkin kasar.

Da sanyin safiyar ranar Asabar da ta gabata Firaministan Lesotho Thomas Thabane dan shekaru 75 da haihuwa, ya tsere bayan sojoji sun mamaye helkwatar hukumar 'yan sanda. Lamari dai ya samo asalinsa ne bayan da Firaminista Thomas Thabane ya sallami babban habsan sojin kasar Tlali Kamoli daga bakin aiki, daga bisani sojojin da ke goyon bayan Mr. Kamoli din suka kai farmaki kan helkwatar rundunar 'yan sanda da gidan firamnistan, lamarin da wasu ke kallo a matsayin yunkuri na juyin mulki.

To sai dai masana irinsu Dimpho Motsamai da ke sharhi kan harkokin tsaro a kudancin Afirka na ganin ba juyin mulki aka shirya yi ba inda ya ke cewar "abin da ya faru a karshen mako ba juyin mulki ba ne, amma zan kira shi wani hargitsi na wasu bata gari da ke zagon kasa ga ikon mahukunta."

Lesotho Maseru Militär Hauptquartier nevorstehende Friedensverhandlungen

'Yan siyasa a Afirka kan zargi soji da yin karan tsaye ga tsarin dimokradiyya a nahiyar.

Shi kuwa Webster Zambara na cibiyar adalci da sasantawa ta birnin Cape Town na kasar Afrika ta Kudu na da akasin tunani don a cewarsa sojojin sun yi yunkuri na kwace madafun iko da karfi tuwo wanda yunkuri ne na juyin mulki karara, inda ya ce "labarin da ya fita cewa sojoji sun mamaye mahimman gine-gine da karbe iko da helkwatar 'yan sanda duk suna nuna matakai ne na juyin mulki."

Firaministan na Lesotho Mr. Thabane dai ya zargi mataimakinsa Mothejoa Metsing da hannu wajen kitsa juyin mulkin, wannan ne ma ya sa ya nemi kungiyar bunkasa tattalin arzikin kasashen kudancin Afirka ta SADC ta tura dakaru zuwa kasar ta Lesotho domin mayar da doka da oda. Rikici a Lesotho dai a iya cewa ba sabon abu ba ne don a cewar Dimpho Motsamai rikicin siyasar kasar ya samo asali daga watannin da aka shafe ana takaddama tsakanin mambobin gwamnatin hadaka da ba sa ga amciji da juna.

Yanzu haka dai shugaban Afirka ta Kudu Jacob Zuma da wakilan gwamnatocin yakin kudancin Afirka sun sanya baki wajen sasanta wannan takkadama da ta kunno kai sai dai ana zuba idanu don ganin irin yadda lamura za su cigaba da wakana a kasar bayan komawar Firaminista bakin aiki.

Mawallafi: Suleiman Babayo
Edita: Ahmed Salisu/USU

Sauti da bidiyo akan labarin