Sabanin kasashen Turai kan ′yan gudun hijira | Siyasa | DW | 17.06.2015
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Siyasa

Sabanin kasashen Turai kan 'yan gudun hijira

Har kawo yanzu kasashen kungiyar sun kasa cimma matsaya guda kan adadin 'yan gudun hijirar da ya kamata ko wace kasa ta dauka.

Matsalar kwararar 'yan gudun hujira na baraza ga kungiyar Tarayyar Turai, inda har kawo yanzu suka kasa cimma matsaya guda kan adadin 'yan gudun hijirar da ta kamata ko wata kasa ta dauka.Ko mi ya sa wasu kasashen ke nacewa a kan batun rarraba 'yan gudun hjirar yayin da wasu ke nuna adawarsu karara, ko kuma mi ya sa aka kasa cimma daidaito kan wannan batu tsakanin kasashen 28 na Tarayyar Turai.

Ga misali kasashen Portugal da Spain na danganta nasu dalillan da yawan marassa aikin yi a kasashen nasu, yayin da kasar Letoniya tace sam bata jin ta shirya. Batun 'yan gudun hijira dai batu ne da ke da sarkakiya, kuma kasar Letoniya ta dandana a shekarun baya inda a halin yanzu kashi 30 cikin 100 na yawan al'ummarta 'yan asalin kasar Rasha ne. gabaki daya dai kasashen kusan goma ne suka ce basu yarda ba da tsarin nan na tilasta daukan 'yan gudun hijirar ta hukumar Tarayyar Turai ta yi.

Da farko dai hukumar ta Tarayyar Turai na son tilastawa kasashen membobi daukan nauyin 'yan gudun hijira a kalla dubu arba'in masu neman mafaka 'yan asalin kasashen Siriya da Erythrea wadanda suka iso kasashen Italiya da Girka tun a ranar 15 ga watan Afrilu da ya gabata. Ana ganin cewa rarraba wannan adadi tsakanin kasashen 28 na Tarayyar Turai, zai taimaka wa kasashen biyu rage cikonson da suke fiskanta ta yadda za su iya fiskantar kwararar bakin hauren da ke shigowa a kullu yaumin ta tekun Baharum ta dalilin rishin zaman lafiya a kasar Libiya.

Fiye da 'yan gudun hijira dubu 60 ne dai suka shigo kasar Italiya ta hanyar teku daga farkon shekara kuma sannu a hankali da dama daga cikinsu sun kurda ta barauniyar hanya zuwa kasashen Girka da ma Turkiya, yayin da hukumar Frontex mai kula da iyakoki na waje na Tarayyar Turai ta kiyasta adadin 'yan gudun hijirar da yawansu ya kai dubu 100 da suka shiga kasashen na Tarayyar Turai ta barauniyar hanya daga farkon shekara kawo yanzu, adadin da ke tayar da hankalin kasashen na Turai kamar yadda Ministan cikin gida na kasar Jamus Thomas de Maiziere ya yi tsokaci a kai.

 "Dangance da matsalar 'yan gudun hijira a Nahiyar Afirka, da kasashen Siriya, ko kuma Iraki kuma bayan abun da ke wakana a tekun Baharum ya kyautu kasashen Turai su samu mafita ta bai daya."

Kawo yanzu dai, kashi 90 cikin 100 na 'yan gudun hijirar da suka gujewa yake-yake ko wasu matsaloli a kasashensu na karkasasu ne a cikin kasashen takwas daga cikin kasashe 28 na Tarayyar Turai. Ska Keller 'yar Majalisa ce ta Tarayyar Turai ta soki batun rishin samun baki guda tsakanin kasashen na Turai kan wannan batu.

 "Ga yadda wasu kasashen membobin Kungiyar Tarayyar Turai ke daukan lamarin kuma suna neman yin watsi da wannan tsari sam abu ne da ba'a san yadda za'a kwatantashi ba.!"

Kasshen Ingila, Island, Danemark suna da nasu tsari na musammen kan batun bada mafaka, kuma suna iya fitar da kansu daga cikin wani sabon tsari rarraba 'yan gudun hijirar. Wasu kasashen suma akalla guda goma cikinsu kuwa har da kasar Faransa sun nuna rishin amincewarsu kan tsarin rarraba 'yan gudun hijirar, inda suke son hana yadda tsarin ke son zama na dindindin, yayin da wasu kasashen da dama suka kasa daukan wani mataki kan batun, don haka a halin yanzu kasashen da ke da wannan buri ba zasu samu adadi na kashi biyu cikin uku da suka dace domin aminta da tsarin rarraba 'yan gudun hijirar na daidai ruwa daidai tsaki.

Sauti da bidiyo akan labarin