1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Sabanin Birtaniya da EU kan batun iyakar Ireland

Gazali Abdou Tasawa
October 15, 2018

Taron EU da Birtaniya kan batun ficewar Birtaniyar daga kungiyar da ya gudana a jiya Lahadi a birnin Brussels ya watse baram-baram ba tare da cimma wata matsaya ba kan batun iyakar Ireland.

https://p.dw.com/p/36XqR
Brüssel Michel Barnier Brexit-Unterhändler mit Nordirland-Vertretern
Hoto: Getty Images/AFP/E. Dunand


Bangarori biyu na Kungiyar Tarayyar Turai da kasar Birtaniya suka kasa cimma daidaito a game da batun shata iyakar kasar Ireland bayan aiwatar da shirin ficewar Birtaniyar daga EU.  

Kasa cimma matsaya a wannan taro wanda ke zama na share fagyen taron kolin kasashen Turai na ranar Laraba mai zuwa ya sanyaya gwiwar bangarorin biyu a daidai lokacin da ya rage kasa da watanni shida wa'adin da aka tsaida na karkare shirin ficewar Birtaniyar daga kungiyar ta EU ya cika. 

Firaministar Birtaniya Theresa May za ta gudanar da taro da ministocinta a gobe Talata domin tattauna batun iyakar kasar ta Ireland da ke zama babban batun da ke kawo tarnaki a cikin tattaunawar da take da kungiyar ta EU da ma kuma a tsakanin mambobin gwamnatin Birtaniyar inda wasu ministocin suka fara yin barazanar yin murabus.