1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Sabani tsakanin kasashen Afirka da kotun duniya

October 14, 2013

Taron shugabannin kasashen Afirka na karshen mako da aka gudanar a birnin Addis Ababa na kasar Habasha, ya nuna karara sabanin da ke tsakanin kasashen da kotun duniya mai hukunta masu miyagun laifuka.

https://p.dw.com/p/19zEd
Hoto: Getachew Tedla HG

Taron shugabannin kasashen Afirka na karshen mako da aka gudanar a birnin Addis Ababa na kasar Habasha, ya nuna karara sabanin da ke tsakanin kasashen da kotun duniya mai hukunta masu miyagun laifuka. Kungiyar ta Tarayyar Afirka ta nemi jinkirta tuhumar da ake yi wa shugabannin nahiyar zuwa lokacin da za su sauka daga kan madafun iko.

Jawabin da ministan harkokin wajen kasar Habasha, Tedros Adhanom, wanda kasarsa ke rike da shugabancin karba-karba na kungiyar Tarayyar Afirka, lokacin bude taron, ya nuna alkiblar da aka nufa a wajen taron.

"Wannan rashin adalci babu wanda zai amince da shi. Haka shi yasa muke nuna damuwa bisa kotun duniya mai hukunta masu laifukan yaki"

Rokon da wasu tsirarun kasashen da suka hada da Kenya suka gabatar na neman ficewar kasashen Afirka daga yarjejeniyar birnin Rome, wadda ta kafa kotun duniya bai samu karbuwa ba. Saboda manyan kasashen nahiyar da ke taka mahimmiyar rawar siyasa, kamar Afirka ta Kudu, da Najeriya, da kuma kasar Ghana sun nuna goyon baya ga kotun ta duniya mai hukunta masu miyagun laifuka gabanin gudanar da taro.

Gipfel Afrikanische Union Addis Abeba GESPIEGELT
Hoto: picture-alliance/dpa

Ministan harkokin wajen kasar ta Habasha Adhanom, ya nemi ganin jinkirta shari'ar da ake yi wa Shugaban Kenya Uhuru Kenyatta, domin ya fuskanci samar da ci-gaba wa kasar. Kenyatta da mataimakinsa William Ruto yanzu haka suna amsa tuhuma a kotun.

Wani matakin da kungiyar ta amince da shi, wanda ake ganin zai janyo cece-kuce shi ne, nan gaba kada wani shugaban kasa ya fuskanci tuhumar bisa miyagun laifuka. Hermen van der Wilt farfesa kan shari'ar kasa da kasa da ke birnin Amsterdam na kasar Netherlands, ya ce haka ya saba wa manufofin kafa kotun:

"Ko kana ofis babu wani dalili da zai kare mutum daga tuhuma ta miyagun laifuka. Ina tsammani manufar kungiyar Tarayyar Afirka shi ne, kauce hakikanin abin da ke faruwa."

Tuhumar da yanzu ake yi wa shugaban kasar ta Kenya Uhuru Kenyatta da mataimakinsa William Ruto ta zafafa mahawarar kan dacewa ko akasin haka, bisa kutsen da ake ganin kotun ta duniya mai hukunta manyan laifukan yaki tana yi wa kasashen Afirka.

Uhuru Kenyatta Ansprache Rede
Hoto: John Muchucha/AFP/Getty Images

Solomon Derso masanin kan lamuran kungiyar Tarayyar Afirka da ke cibiyar lamuran tsaro a birnin Addis Ababa na kasar Habasha, ya ce, bukatar da kungiyar ta AU ta gabatar wa Kwamitin Sulhu na Majalisar Dinkin Duniya bisa dakatar da shari'ar da ake yi wa shugaban Kenya Keyatta, karkashin kudiri na 16 na yarjejeniyar birnin Rome, zai yi wuya a amince. Sannan ya yaba da matakin ci gaba da zaman kasashen cikin yarjejeniyar da ta kafa kotun ta duniya:

"Babu gagarumar ficewa wanda abu ne mai kyau. Amma daga bangaren bukatar da suka nema ta tsame shugabannin da suke mulki daga fuskantar tuhuma, a gaskiya zai yi wuya a cike gibin da ke tsakanin kungiyar Afirka da kotun duniya, wanda aka samu cikin shekarun da suka gabata."

Duk da rashin ficewa daga cikin yarjejeniyar, amma shugabannin kasashen Afirka sun nemi dakatar da tuhumar kan duk wani shugaban da ya ke rike da madafun iko.

Mawallafi: Suleiman Babayo
Edita: Umaru Aliyu