Sa-in-sa tsakanin Rasha da Turkiya | Labarai | DW | 31.01.2016
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Sa-in-sa tsakanin Rasha da Turkiya

Ma'aikatar tsaron Rasha ta musanta zargin da Turkiyya ta yi na keta sararin samaniyarta a jiya Asabar bayan da jirgin yakinta ya yi shawagi a wani bangare na kasar.

Mai magana da yawun ma'aikatar tsaron Igor Konashenkov Rasha din ya ce wannan zancen ba shi da tushe balle makama, hasalima wata farfaganda ce kawai Turkiyya ke yadawa.

Shugaban Turkiyya Recep Tayyib Erdogan ya ce muddin Rasha ba ta kauracewa yi mata kutse cikin sararin samaniyarta to za ta dau mataki.Shugaban kungiyar tsaro ta NATO Jens Stoltengerg ya shawarci Rasha da ta mutunta dokokin da aka shimfida dangane da batun da ya dangaci sararin samaniya na kasashe da ke cikin kungiyar ta NATO.