1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Amirka ta yi kasheidi ga Iran

Ramatu Garba Baba SB
July 23, 2018

Shugaba Donald Trump na Amirka ya gargadi Shugaba Hassan Rouhani na Iran kan cewa ya daina yi wa kasarsa barazana ko kuwa ya fuskanci matsanancin hukuncin da babau wata kasa da ta taba fuskanta a tarihi.

https://p.dw.com/p/31vnr
Bildkombo Donald Trump und Hassan Rohani
Shugaban Amirka Donald Trump da Shugaban Iran Hassan RouhaniHoto: Getty Images/AFP/N. Kamm//A. Kenare

Shugaba Donald Trump ya mayar da martani ne bayan da shugaban na Iran Hassan Rouhani ya nemi Amirka da ta bi a hankali don gudun haifar da mummunan rikici da zai kasance babbar barazana ga zaman lafiya a duniya, domin a cewar Rouhani, ya dace Amirka ta fahimci mahimmancin tasirin zaman lafiya da Iran, inda ya kwatanta Iran a matsayin ginshikin zaman lafiya a duniya. Batun dai ya haifar da dambarwa inda masu sharhi ke fassara kalaman shugabanin biyu bisa fahimtarsu. Jamshid Barzegar shi ne shugaban sashen harshen Parisanci na Iran na tashar DW, ya yi tsokaci kan illar furta irin wadannan kalaman a daidai wannan lokaci ya na mai cewa:

''A zahiri ba mu san abin da duk wannan zai haifar ba, amman ai mun fara ganin illar musayar kalaman ganin yadda ya shafi tattalin arzikin Iran idan aka yi la'akari da faduwar darajar kudin kasar a kasuwar hada-hadar hannayen jari, daga karshe ma Iran ba ta da zabi face ta koma kan teburin sulhu.''

Jamshid Barzegar -  neuer Leiter der DW Farsi-Redaktion.
Jamshid Barzegar shugaban Sashen Parisanci na DWHoto: DW/B. Scheid

Tsahon lokaci na cacar baki

Shekara da shekaru kenan Amirka da Iran ke yi wa junansu barazana kan matakin da za su iya dauka don ladabtar da juna, a lokuta da dama karfafa takunkumi kan Iran shi ne abin da Amirka ke ikirarin yi, sakataren harkokin wajen kasar ta Amirka Mike Pompeo ya nemi hadin kan kasashen da ke da sabani da Iran wajen daukar matakin da zai zama babban hukunci ga Tehran yana mai cewa: 

''Muna kira ga sauran kasashen duniya da suka kosa da munanan halayen Iran su zo mu hada karfi domin hana kasar duk wata dama, ta hanyar kakaba mata takunkumin karya tattalin arziki da duk wata nutsuwa da ke iya bata damar gudanar da ayyukan ta'addancinta a sassan duniya.''

Mike Pompeo
Sakataran harkokin wajen Amirka Mike PompeoHoto: picture-alliance/AP Photo/M. J. Terrill

Batun lallabar Iran kan ta yi watsi da shirinta na  nukiliya ya kasance babban kalubale ga gwamnatin Shugaba Hassan Rouhani duk da cewa an sami ci-gaba a can baya da wasu kasashen duniya biyar suka cimma yarjejeniya da kasar kan ta jingine shirinta na nukiliya, yayin da a hannu guda aka sassauta takunkuman da aka aza mata. Sai dai Shugaba Trump ya janye kasarsa ta Amirka daga cikin yarjejeniyar wanda wasu masana ke ganin jan ra'ayinsa kan komawa kan teburin sulhu zai iya zama dabarar jan lokaci har a nemo bakin zaren warware takaddamar.