Rwanda ta janye ′yan tawayen Kongo daga kan iyakarta | Labarai | DW | 03.04.2013
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Rwanda ta janye 'yan tawayen Kongo daga kan iyakarta

Hukumomin Rwanda sun dauki matakin janye mayakan 'yan tawayen Kongo daga kan iyakarta domin mutunta yarjejeniyar da kasashen biyu suka cimma a kan zaman lafiya.

Rahotanni daga Kigali fadar gwamnatin Rwanda sun tabbatar da janyewar daruruwan sojojin 'yan tawayen kungiyar M23 daga kan iyaka da kasar jamhuriyar demokradiyar Kongo.
Akalla 'yan tawayen da Kigali ta bayyana a matsayin tsaffin mayakan kungiyar da Bosco Ntanganda ke wa jagoranci, mutumin da ya ba da kansa ga kotun hukunta manyan laifuffukan yaki ta duniya wato ICC, sun kai ga 682 wadanda suka tsallaka kan iyakar kasar da ta Kongo. Da ma dai an jima ana zargin kasar ta Rwanda da taimaka wa mayakan kungiyoyin 'yan tawayen Kongo.
Wannan matakin na zuwa ne bayan da Majalisar Dinkin Duniya ta bayyana bukatar baiwa dakarun kiyaye zaman lafiya da ke karkashinta karfin kafa wata runduna ta musamman da za ta iya gwabza fada da duk wani gungun mutane a yankin musamman a kasar ta Kongo.

Mawallafi: Issoufou Mamane
Edita: Mohammad Nasiru Awal