Rwanda: Shugaba Kagame ya yi hasashen nasara | Labarai | DW | 01.08.2017
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Rwanda: Shugaba Kagame ya yi hasashen nasara

Shugaba Paul Kagame na kasar Ruwanda ya ce zai lashe zaben kasar karo na uku da yake takara, yana mai tabbatarwa 'yan kasar cewar kasar za ta ga sauye-sauye ta fuskar arziki.

Cikin wannan mako ne dai aka tsara yin zaben shugaban kasa a kasar wadda ke zama cikin kananan kasashen yankin gabashin Afirka. Mr. Kagame wanda ke mulkin kasar shekaru 17 a yanzu, ya yi nasarar samun tsayawa takara karo na uku ne bayan sauya tsarin mulkin kasar a shekara ta 2015, a zaben raba gardamar da kasashen duniya suka aza ayar tambaya a kansa.

Ana dai kallon ta yiwu shugaban na Ruwanda mai shekaru 58 na iya zama bisa karaga kar i zuwa shekara ta 2034, shubanan da aka yaba wa kokarin kyautata al'amuran kasar bayan kisan kiyashin da ya halaka kimanin mutane miliyan guda cikin  shekara ta 1994.