Ruwanda ta sallami manyan hafsoshin tsaronta
September 1, 2024Talla
Shugaban kasr ta Ruwanda Paul Kagame, ya amince da murabus din Janar Jean Bosco Kazura da karin wasu sojoji dubu da 162 masu sauran mukamai.
Shi dai Janar Kazura, mai shekaru 62, kafin murabus din nasa, shi ne hafsan hafsoshin kasar, mukamin da ya rike tsakanin shekarar 2019 zuwa 2023.
Haka nan ma ya taba zama mai bai wa shugaba Kagamen shawara kan harkokin soja, sannan ya jagoranci rundunar kiyaye zaman lafiya ta MDD a Mali a tsakanin 2013 zuwa 2014.
Shi dai Shugaba Paul Kagame, ya zargi sojoji da dama ne da rashin da'a, abin kuma da ya sanya shi daukar matakin a cewarsa.